LABARAI/NEWS

Hukumar EFCC. Ta chafke Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Hukumar EFCC. Ta chafke Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha


hukumar EFCC din dai Tun sanyin Safiyar Yau ne suka mamaye gidan da jami’an tsaro misalin karfe 11 na safe.

Jami’an tsaro sun zagaye gidan Sanata Okorocha dake ynguwar Maitama dake Abuja, sannan sun rika harba barkonon tsohuwa ga magoya bayan Okorocha a gidan sa a lokacin da suka kawo mamya gidan.

Sai dai kuma a lokacin da jami’an tsaro ke kokarin fito da Okorocha daga gidan sa ya tattauna da manema labarai in da ya ce” A na nema na ne ruwa ajallo domin a hana ni halartar zaman tantance ƴan takarar shugaban kasa da za ayi na jam’iyyar APC.

” Ba su so in halarci wannan zama. Shine ya sa suka aiko jami’an tsaro su zo su kama ni. Wannan shine kawai dalili amma babu wani abu bayan haka.

Sai dai kuma jami’an hukumar EFCC sun ƙaryata haka inda suka ce Okorocha ya tsallake belin kotu har sau biyu.

” Kotu ta yi zama domin sauraren karar da aka shigar akan sa amma a duk lokacin da aka bukaci ya bayyana a kotu sai ya ki zuwa. A karshe dai dole alkalin kotun ya ke ɗage zaman kotun.

” Da muka gaji da boye boyen da yake yi shine muka kama shi domin ya zo yayi mana bayani game da zargin wawushe biliyoyin kuɗaden talakawan jihar Imo da yai a lokacin ya na gwamna.

Shi dai Okorocha ya Hakikan ce cewar Siyasa ce ta kokarin hana shi bayyana cikin Yan takaran APC domin tsoron da ake da shi na raayin sa na kin Amince wa da Dauki dorin da jami’iyar ke son yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button