Nishadi

Hukumar tace fina finai ta Hana Rarara sakin waka a jihar Kano sai an …

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano ta Hana mawakin siyarsar Nan dauda kahuto rarara sakin waka a jihar Kano har sai an tace wakar

Hukumar ta bakin Mai magana da yawun su ya tabbatar da wannan umarni inda yace an Hana duk wani mawaki sakin wakar sa har sai hukumar tace fina finai ta tace wakar sa

Wannan dai ya biyo bayan tsamar da mawakin yake Yi da ganduje Wanda har ikirarin rushe masa gida sai da akayi don razana shi

Idan Batu manta ba dai an kama sarkin wakar sarkin Kano murabus naziru m Ahmad sakamakon wakr da ya saki ba tare da hukumar tace fina finai ta tace ta ba

Wannantasa sarkin wakar ta tsinci kan sa a gidan yari inda daga bisani aka sake shi Kuma aka Yi masa gargadin kar ya sake sakin wakar har sai an tace ta

Haka Kuma Ado Gwanja Shima a Yan kwanakin baya hukumar ta gargade shi da sakin wakar sa Amma sai mawaki ya gudu jihar legas inda ya saki wakar tasa a chan Wanda ta marukar girgiza mutane

Shi ma dauda kahuto rarara Yanzu haka ya tsinci kan sa a cikin jerin manyan mawakan arewacin Nigeria Wanda hukumar ta tace fina finai ta umarta da kada su sake sakin waka ba tare da an tace ta ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button