Fadakarwa

HUKUNCIN TAFSIRIN MACE DA SANYA SHI A GIDAN TV.

HUKUNCIN TAFSIRIN MACE DA SANYA SHI A GIDAN TV.

TAMBAYA ?
ﻫﻞ ﻳﺠﻮﺯ ﻟﻠﻤﺮﺃﺓ ﺃﻥ ﺗﻌﻠِّﻢ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺑﺼﻮﺗﻬﺎ ؟
Shin ya Halatta ga Mace ta Karantar da Maza da Mata da
Muryarta ?
AMSA
ﻛﻮﻥ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻳﺘﻌﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﻛﻮﻥ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻳﺘﻌﻠَّﻤْﻦَ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺟﻞ
ﻣﻤﺎ ﻻ ﻣﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﺷﺮﻋًﺎ، ﻭﺻﻮﺕ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻟﻴﺲ ﺑﻌﻮﺭﺓ ﻓﻲ ﻧﻔﺴﻪ، ﻭﺇﻧﻤﺎ
ﺍﻟﻌﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺨﻀﻮﻉ ﺑﺼﻮﺗﻬﺎ، ﻭﺍﻟﺘﺮﺧﻴﻢ ﻟﺼﻮﺗﻬﺎ، ﻟﻘﻮﻟﻪ – ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﻓَﻠَﺎ
ﺗَﺨْﻀَﻌْﻦَ ﺑِﺎﻟْﻘَﻮْﻝِ ﻓَﻴَﻄْﻤَﻊَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻲ ﻗَﻠْﺒِﻪِ ﻣَﺮَﺽٌ، / ﻟﻜﻦ ﻣﻊ ﺫﻟﻚ ﻟﻢ
ﻳﺸﺮﻉ ﻟﻠﻤﺮﺃﺓ ﺃﻥ ﺗﺆﺫِّﻥ، ﻭﻻ ﺃﻥ ﺗﺼﻠﻲ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ، ﻭﻻ ﺃﻥ ﺗﺨﻄﺐ
ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻭﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ، ﻭﻻ ﺃﻥ ﺗﺴﺒﺢ ﺇﻥ ﺃﺧﻄﺄ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺑﻞ ﺗﺼﻔﻖ .
‏[ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ‏( 17 /202 ، 203 )]Kasantuwar Maza su Nemi Ilimi daga Gurin Mace, da
Kasantuwar Mãta su Nemi Ilimi daga Gurin Maza, Yana daga
Cikin Abin da Shari’a Bata Hana ba. Kuma Sautin Muryar Mace
ba Al’aura bane Akaran Kansa. Abin da Shari’a ta Hana A
Muryar Mace Shi ne: Kashe Muryarta ta hanyar Rausaya da
Shagwaɓa ga Wanda ba Mijinta ba. Saboda Faɗin
Allah Ta’ãla:
ﻓَﻠَﺎ ﺗَﺨْﻀَﻌْﻦَ ﺑِﺎﻟْﻘَﻮْﻝِ ﻓَﻴَﻄْﻤَﻊَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻲ ﻗَﻠْﺒِﻪِ ﻣَﺮَﺽٌ
‏[ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ ﺍﻵﻳﺔ ‏( ٣٢ )]Sai dai Kuma Duk da Haka, Ba’a Shar’anta wa Mace Kiran
Sallah ba, Haka ba’a Yarda ta Jagoranci Maza Sallah ba, Haka
Ma Kuɗubar Juma’a da ta Sallar Idi, Haka Ba’a Yarda Tace
(Subhanallahi) Idan Liman yayi kuskure a Sallah ba, Sai dai tayi
masa ishara ta hanyar tafi da hannu.
TAMBAYAR DA AKAYI WA SHEIKH BIN-BÃZZ (RH)
ﻣﺎﺫﺍ ﺗﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻦ ﻇﻬﻮﺭ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻠﻔﺰﻳﻮﻥ ؟
Meye Zaku Ce game da Bayyanar Mata A Gidajen TV ?
AMSA
ﻇﻬﻮﺭﻫﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻠﻔﺰﻳﻮﻥ ﻣﺘﺤﺠﺒﺎﺕ ﻣﺴﺘﻮﺭﺍﺕ ﺍﻟﺒﺪﻥ ﻭﺍﻟﻮﺟﻪ ﻓﻲ
ﺧﻄﺒﺔ ﺃﻭ ﻓﻲ ﻛﻼﻡ ﺃﻭ ﻓﻲ ﺗﻮﺟﻴﻪ ﻭﺇﺭﺷﺎﺩ ﺃﻭ ﺇﺧﺒﺎﺭ ﻋﻦ ﺷﻲﺀ، ﻓﻼ
ﻳﻀﺮ، ﻳﺠﻮﺯ ﺫﺍﻟﻚ .
Bayyanarsu A Gidajen TV Sanye da Hijabi da Sutarar da ta Rufe
Jiki da Fuska, Don Gabãtar da Wata Nasiha, Ko Magana akan
Wata Matsala, Ko Yin Nuni akan Wani Abu, Ko bada labarii
game da faruwar wani abu, Wannan Babu Matsala,Ya Halatta.
Akwai Zantuka da yawa Na Malaman Sunnah akan Halaccin
Mace ta Karantar da Al’ummah a gidanta ko a Kafar Sada
zumunta a bisa tsarin Shari’a.
Copied.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button