LABARAI/NEWS

Ibrahim Zazzaky Shirgegen Makaryaci Ne, Cewar Malamin Shi’a Hamza Lawal

Ibrahim Zazzaky Shirgegen Makaryaci Ne, Cewar Malamin Shi’a Hamza Lawal

Daga Indabawa Aliyu Imam

Fitaccen Malamin Shi’a a Najeriya Malam Hamza Lawal ya caccaki Ibrahim Zazzaky yana mai cewa mutum ne makaryaci mai son duniya da mulki.

Hamza wanda tsohon dalibin Zazzaky ne ya kuma bayyana Zazzaky a matsayin wani mutum mai matacciyar zuciya wanda ke son a girmama shi fiye da yadda ya cancanta.

“Zazzaky ne saboda tsabar karyarsa idan yana zaune da mutane sai ya tashi ya shiga wani wuri, idan ya dawo sai ya ce wai Imam Mahdi ne ya kawo masa ziyara suka gana.” A cewar Hamza Lawal.

Ya kuma ce da kunnensa ya ji Zazzaky ya shirga wata karya a ranakun Kudus cewa suna da wata Kyamara wacce ke zuko adadin cincirindon mutane tare da lissafa adadinsu har ta kure lissafinta amma ba ta iya lissafa mutanensa ba, yana alfahari da bugun kirji da wannan.

Kana Malam ya ce Zazzaky ya sa mabiyansa sun mayar da shi kamar Ubangiji, ta yadda suke kashe kawunansu ta dalilinsa, ya bukaci Zazzaky da ya gaggauta fitowa ya tubar wa Allah bisa ikrarinsa na cewa muddin aka taba shi Najeriya ba za ta zauna lafiya ba duba da dubban mabiyan da yake da su. Wanda hakan ne ya yi silar mabiyansa suka nemi rigima da sojoji a watan disambar shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Ko a kwanakin baya an ga Zazzaky a wani bidiyo yana mai cewa Sojoji sun harbe shi a ido, wanda ta kai idon nasa ya fado kasa amma ya dauke shi ya yi addu’a ya mayar da shi, kuma ya zauna ras har ma yana ganin komai lafiya lau. Wanda jama’a da dama suka yi masa martanin cewa labarinsa ba gaskiya ba ne don ya sa’ba da hankali.

Tun da jimawa Malaman da ke adawa da Malam Zazzaky suka bayyana maganganunsa cewa karairayi ne. A cewarsu ya sha kirkirar karya ya zantar da ita don ya ‘bata sahabban Annabi da matansa wanda idan za a kashe shi ba zai iya nuna labarin ko ingancinsa a littafan tarihin musulunci ba. Malam Zazzaky sun kuma ambace shi cewa mutum ne mai raunin ilmin addini wanda ko ba’kin karatu ba ya iya ja daidai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button