Islamic Chemist

Idan kana so kullum matarka tana sha’awar jima’i da kai da tsawon lokacin da zaka

Wani abu da yawancin maza basu sani ba shi ne yawan lokacin da ya kamata kayi akan matarka a yayi gudanar da jima’i da ita.Duk da yake babu wani bincike daya tabbatar da hakikanin tsawon lokacin da magidanci zai dauka akan matarsa yana jima’i da ita.

Sai dai kuma binciken ya tabbatar da cewa, mafi karancin lokacin da namiji zai yi yana jima’i da matarsa shi ne daga mintuna 3 zuwa 7, duk bamijin da ya kasa daukar wannan lokacin yana saduwa da matarsa to tabbas yanada matsalar daya kamata yaga likita.

Haka zalika mintuna 7 zuwa 13 sune tsawon lokutan da idan namiji yayi a lokacin saduwa da matarsa bai takurawa matarsa ba, shi ma kuma bai jigata kansa ba, kamar yadda bincike ya nuna.

Kamar yadda nazarin ya kara tabbatar da cewa, mintuna 10 zuwa 30 akan mace ana jima’i da ita lokuta ne da suka wuce hankali ga maza masu irin wannan jimawan akan matansu.

Sai dai wadannan tsawon lokutan basu hada da lokutan wasannin motsa sha’awa ba, ana lissafin lokutan ne daga lokacin da shi maigida ya shigar da azzakarin sa farjin matarsa.Babban abunda ya kamata maza magidanta su fahimta anan shine,

ba wai ana nufin cewa dole ne sai maza sun dauki tsawon wadannan lokutan akan matansu ba, ko kuma su takaita kamar yadda binciken ya nuna ba.Abun da ya kamata maza su fahinta shine ana bukatar kowani magidanci ya iya fahimtar tsawon lokacin da matarsa take iya samun gamsuwa a lokacin jima’i.

Wasu matan a cikin mintuna biyu kacal sun biya bukata, akwai matan da kuma a lokutan wasannin motsa sha’awa ma sun kawo, kamar yadda ake samun wasu matan muddin ba’a daukan sama da sa’a guda ko rabin sa’a ana gurzarsu ba basusan ma anayi ba.

Masana sun bada shawaran kan cewa, ko wani magidanci dole ne ya fahimci matarsa sosai a jima’ince ta haka ne kawai zai iya gamsar da ita babu cuta babu cutarwa.Ganin shi gamsar da mace a yayin jima’i dole ne akan dukkannin wani magidanci.

Ga mazan da suke yin shaye shaye kamin suyi jima’i suna iya fuskantar Matsalolin ko dai a kamin tsufan su ko bayan tsufan su.Ita mace ba wai tsawon lokacin da aka dauka akanta shine ke sata gamsuwa ba, Kawai magidanci yayi kokarin gano abubuwan da suke saurin gamsar da matarsa.

Wasa da ita ne ko kuma saduwa da ita ke sata gamsuwa da wuri, a saduwa da ita dinma a wani yanayin kwanciyar jima’i take samun gamsuwa.

Wadanan sune abubuwan da maigida zai gano amma bawai sai yayi shaye shaye ba domin gamsar da matarsa.

Sai dai babu laifi lokaci zuwa lokaci namiji ya sha maganin da zai kara masa lafiyar gaba ko karin Kuzari, amma kada kuma ya zame masa idan bai sha wani abun da ya saba sha ba bazai iya gamsar da matarsa ba.Allah yasa mu dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button