Daga Malaman mu

ILIMI KYAUTAR ALLAH

ZANCEN ZUCI…(74).

ILIMI KYAUTAR ALLAH..!!!

 

Idan ka kalli rayuwa da idon basira tare da zurfafa tunani za ka fahimci cewa- duk duniya- babu abun da yakai darajar tafiyar da rayuwa a kan harkar ilimi da kira zuwa ga Allah, tare da neman yardar Allah shi kad’ai bisa koyarwar Manzon rahama S.A.W.

 

Irin wannan rayuwar itace rayuwar da babu nadama a cikinta. Hasali-ma albarkar ta kullun naso take qara yi a tsakanin al’umma. Musamman idan kayi la’akari da tasirin ilimi wajen sanar da mutane Allah da yadda za su bauta masa shi kad’ai. Wannan shi ne babban jari wanda ba ya yankewa.

 

Bayan ni’imar musulunci; duk wata ni’ima komin girmanta ; da zarar ni’imar ilimi ta bayyana sai kaga wancan ta koma sahun baya.

 

Tafiyarka a wannan rayuwar tana fitar da sawun qafarka. Kayi qoqari idan ka wuce wata rana ace sawun alheri sun taba bi ta nan. Amma ka sani sawun masu ilimi ya fi dad’ewa a bayan qasa.

 

Allah Ka azurtamu da ilimi mai amfani mai albarka. Ka bamu ikon yad’a ilimi bisa tafarkin Manzo S.A.W. Ka yarda damu da ayyukanmu. Allah Ka haskaka makwancin Dr. Ahmad BUK da sauran malamai ma su daraja. Ameen.

 

Jameel Muhammad Sadis

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button