Islamic Chemist

ILLAR JINKIRTA FITSARI ALHALIN KANAJIN FITSARIN:

ILLAR JINKIRTA FITSARI ALHALIN KANAJIN FITSARIN:

  1. Kidney Stone: rike fitsari a mara ya na haifar da cutar koda da ake kira ‘kidney stone’ a turance.
  2. Damage to pelvic floor muscles: ya kan rage karfin bangaren jikin da yake hana fitsari fita a kowani lokaci wanda ake kira da ‘Pelvic Floor muscles’. Idan wannan guri ba shi da karfin, mutum zai dinga digar da fitsari a koda yaushe.

3- Bladder stretching: ya kan sa mafitsara (bladder) ta girma kamar balam balam waanda hakan zai aifar da mutum yana jin fitsari ammaa idan yaje ya zauna fitsari baya fita.

4- Urinary Tract Infection : yakan kawo bawa kwayar cuta Daman zama a mafitsara Wanda yakan zuwa da alamomi kamar haka Ciwon mara, zafi lokocin fitsari, rashin samun fitsari sosai.

5- Interstial bladder: yakan kawo matsalar ciwon mafitsara mai sanani wanda yakw zuwa da takura idan an zauna fitsari.

6- Kidney damage : idan fitsari ta cika mafitsara zaibi hanyar ta koma kidney wanda hakan zai lalata kidney gabaki daya.

7- Incontinence : yakan iya kawo matsalar yoyon fitsari lokocin da mutum yana dariya ko tari.

8- Urine retention: zai sa hanyar fitsari ta toshe hakan ta hana fitsari fita gaba Daya , kafin fitsari tafita sai ansawa mutum hanyar fitsari na roba.

HALAYYA GUDA 8 DA YAKE KAWOWA ODA (KIDNEY) MATSALA :

Matsalar oda (Kidney) tayi yawa a kasar mu Najeriya to ga kadan daga cikin halayyar mu da take kawo matsalar:

1- Rashin shan isheshshen ruwa.
2- Rike fitsari a mafitsara sai ya takura maka.
3- Amfani da manda/gishiri diyawa.
4- Yawan amfani da magungunan dauke ciwo.
5- Yawan cin abinci masu gina jiki (proteins).
6- Yawan shan barasa (giya).
7- Yawan amfani da sinadaran caffeine.
8- Sai kuma rashin isheshahen bacci.

Lafiya uwar jiki

Kuyi Share sabida wassu su amfana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button