Latest Hausa Novels

ILLAR QIN BIYAN BASHI

ILLAR QIN BIYAN BASHI


Cin bashi Qaskanci ne, kuma cikinsa akwai damuwa, akwai bakin ciki da rashin barci.

Da yawa zaka ga mutum yaci bashin mutane, yana da halin biya amma yaqi ya biya saboda ganganci da bushewar zuciya. Wasu ma ko kayi musu “Allah ya isa”. Ba zasu damu ba.

Idan mutum ya mutu da bashi akansa, Allah zai sanya Mala’iku su daureshi da sasari wato sarkoki (chains) na wutar jahannama.

Ahaka zai kasance acikin Qabarinsa cikin wahala da Qunchi da azaba. Ba za’a kunceshi ba, sai ranar da danginsa suka biya masa wannan bashin, ko kuma masu bashin suka yafe masa.

Kuma za’a sanya katanga tsakaninsa da duk wata addu’ar da Muminai zasuyi masa. Addu’ar ba zata riskeshi ba, sai ranar da danginsa suka biya masa basussukan da ake binsa.

Ko shahada mutum yayi awajen yaqi, Annabi ﷺ yace za’a tsareshi bazai shiga Aljannah ba, har sai an biya masa bashin da ake binsa.

An kawo gawar wani Sahabi agaban Annabi ﷺ domin yai masa sallah. Har ya mike zai masa sallar sai ya tambaya ko ana bisa bashi? Suka ce eh ana binsa dirhami biyu.

Manzon Allah ﷺ yace kuyi masa sallah, Ni bazan yi masa sallah ba”. Bai masa sallah ba, har sai da wani Sahabin ya dauki alkawarin cewa zai biya masa.

‘Yan uwa ku guji yawan cin bashi, irin na ba gaira babu dalili din nana, domin baku san yaushe ne za’a dauke ranka ba. Kada kaje ka mutu alhali ana binka bashi.

Idan kasan ana binka bashi, yi kokari ka rubutashi akan takarda acikin wasiyyarka, koda “Ta-Allah” zata kasance. Sannan da zarar ka samu damar biya kaje ka biya mutane hakkinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button