Islamic Chemist

ILLAR SHAN AMPICLOX BA BISA KA’IDA BA

ILLAR SHAN AMPICLOX BA BISA KA’IDA BA
๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š๐Ÿ’Š

AMPICLOX wannan wani magani ne da ya shahara wanda mutanen mu sun bude ido dashi matuka. Zaka samu koya mutum ya sami rauni kurum zai tafi Chemist yace abashi AMPICLOX haka zaizo yaita shaโ€ฆ baimasan kaidojin shansa ba ko kadanโ€ฆ.

Haka zaita faman dirkawa cikinsa, idan yaga ankwana biyu babu canji a ciwon ya kuma komawa yace abashi wanda yafi kowanne karfi wato BEECHAMโ€ฆ. saboda kurum damuwarsa yaga ciwon ya warke kota halin yaya.

Wannan magani ba abun wasa bane. Broad spectrum antibiotics ne, ko da matsalarka ta shafi antibiotics ba likitan dake dora mara lafiya kan Broad spectrum antibiotics masu karfi irin haka nan takeโ€ฆ mu kan mu da narrow spectrum muke fara treatment sai abun yaci turaโ€ฆ

Duk ma’aikacin lafiyar dake dora mara lafiya akan broad spectrum kai tsaye toh baima san me yake ba. Ballantana kuma kai kanka da sunan kurum ka rike.

Akaf bayanin maganin AMPICLOX ka duba kowacce irin journal a duniya bazaka ta6a ganin anrubuta cewa wannan maganin yana taimakawa wajen kamewar ciwo ba, ko kuma yana magance rauni (wound) ba, bazaka ta6a gani ba. Amma mutanen mu kunqi ku gane duniya anwaye. Komi kunfison shi ai muku kuna daga kwance bazaku asibiti ba. Shyasa cuttuka sukafi yiwa mutanen kisan wulakanciโ€ฆ๐Ÿ˜ฅ

Abunda bai kamata yai ajalin mutanen mu bama yanzu kashemu yakeโ€ฆ..

Inbanda Nigeria bama kasar da zakaje chemist ko pharmacy store kace abaka ANTIBIOTICS batare da Prescription sheet na likita tare da license number dinsa ba ajiki abakaโ€ฆ. Wannan kuma shike cutar da jama’a dinmu domin kuna yiwa kanku illa baku damu kusan kunayi ba.

Antibiotics ana amfani dasu wajen magance ciwon da kwayoyin bacteria suka haddasa, kai ciwo kurum kaji inda abunda kafi bukata baifi Vitamins supplement ba da zasu taimakawa Clotting factor dinka a lokacin jini ya zamto ya tsaya.

Ana karawa mutum da antibiotics ne idan akaga ciwo ya nuna alamun infection ma’ana kwayoyin cuta sun hau kai, kila har ya fara ruwa, ko ya fara wariโ€ฆ. kuma ko a irin wannan halin AMPICLOX bashi ne magani a za6in farko ba.

Likitoci matakin farko sai mun duba yama immunity dinka yake, shin baka da Allergy ma da irin wannan antibiotics din, sannan mui nazari muga shin wacce irin bacteria ce tafi kusa da kama wannan sahin jikin naka inda ciwon yake.

Bayan mun auna wannan abu nagaba, shine ita bacteria wacce irice? Wanne jinsi take (Gram+ve ko Gram -ve), Shin me sakin guba ce (toxins) ko kuwa? Shin tana son iska (aerobic) ko bame rayuwa a inda iska take bace (anerobic)? Ko kuwa takan iya rayuwa walau da iska ko ba iska (microerophilic) Shin tana da jijiya ko bata da jijiya (cell wall)? shin kwana nawa takanyi kafin ta mutu? Shin magani bactericidal me kisa, ko kuwa antimicrobials me rage mata karfi ya dace mu fara amfani dashiโ€ฆโ€ฆ. Da sauran abubuwa masu yawa da basai na lissafa muku su baki daya ba. Wannan shine matakin farko

Sannan in munzo rubuta magani, sai mun duba tsakanin mace da namiji nan ma akwai bambanci, Nauyinka nan ma abun dubawa ne, shin yaya baka da hypersensitivity, bayan wannan shin baka da ciwo da kake shan maganinsa wanda bai bukatar agaurayashi da wannan antibiotics misali maganin hawan jini, malaria, ciwon koda, ciwon suga, asthma da sauransuโ€ฆ..

Sannan maganin awa nake yaje rabin rayuwarsa ajika (half life), DOSE nawa ya dace dakai bisa nauyinka da shekarunka acikin jikinka, shin a ina ma ake narkar dashi wannan magani da muke shirin baka? Shin baka da matsala ta gurin da ake narkar dashi ko ake tacesa ya fita (Excretion)? Metabolism (huhu, hanta, koda ko hanji) duk gurare ne da magunguna daban daban ake iya metabolism dinsuโ€ฆ..

Sannan shin abincin da kake ci ma ya dace ahadasa da irin wannan maganin ko kuwa? Shin kafin aci abinci ko bayan anci abinci ya dace asha ko kuwa?, shin baka ma da ulcer aciki ko yaya?
Duk wadannan abubuwa ne da muke nazarinsu kafin dora mutum akan magani, shyasa da wuya mutum yaje ga likita kaga ciwo yaci gaba da lalalatashi.

Idan kuwa muka baka maganin da muke tunanin shine amma bawani canji toh a irin wannan ne sai mun turaka ga LAB SCIENTIST sun dau sample din ruwan dake fita agurin domin sui CULTURE AND SENSITIVITY su gano mana wacce irin kwayar cuta ce, sannan wanne magani ne zai halaka ta. Ba daka muke ba.

๐Ÿ’”
Amma kowa kurum yaji ciwo ba ruwansa AMPICLOXโ€ฆ toh bari kuji illolin hakan

 1. Shan wannan maganin dakayi kasani kangarar da jikinka kake gaba kiri kiri Antibiotics zaizo yaki aiki ajikinka! abunda muke kira resistance. Saboda ka saba Abusing din antibiotics anyhow duk randa wani ciwon ya kamaka koda maganin da ake baka shine zai warkar dakai toh zakaita sha kuwa kaqi warkewaโ€ฆ zakaci wahala.

Wannan ita tasa da yawa cikin mutane sai kaji mutum yazo yana surutun yaje asibiti anbashi magani amma sai sha yake shi bawani canjiโ€ฆ likitan ma baisan me yake ba. Kaine bakasan me kakeyi baโ€ฆ.. Saboda bakasan cewa kai kaima kanka da kanka illar ba ta hanyar shan maganin antibiotics abaya daka wanda ka sabawa kanka, kaga ko ai dole kaci wahala

 1. Kana lalata lining din cikin uwar hanjinka ne, ana nan zaka hadu da Pseudomembranous colitis watarana! wato hanjinka zai ta6u ka rika fama fa zafin ciki koma kaji shiru ka dauka komi normal sai rana tsaka aji ance wane ya mutu ba ciwo ba komi.

A domin me? Sanine ba aiba, kaine kaima kanka illar da anhankali hanjinka yakai ga hujewaโ€ฆ. kashinka wanda yake kunshe da milyoyin bacteria ya zuba cikin kayan cikinka ya haddasa sepsis wanda hakan yakai ga peritonitis ka mutu nan takeโ€ฆ

Akasashen da akaci gabane da suka damu susan abunda ya kashe mutum da ake kawomana gawa mui AUTOPSY bayan mun bude kayan ciki mukan iya gano irin abun ya faru kenan da mutum har ya mutu. Mu kuwa saide atafi a hargitse mutum acikin kasa shikenan tasa ta qare kuma.

 1. Duk randa amai da gudawa suka kama me irin shan antibiotics din toh nan ma ka kuka da kankaโ€ฆ kafi kowa saurin chance din mutuwa
 2. Zaka iya haduwa da lalacewar fata.
 3. Zaka iya haduwa da ciwon hantaโ€ฆ wanda sai akarshe zai bayyana. Nasha fadamuku ba iya Hepatitis virus ne ke haddasa ciwon hanta ba, hatta paracemol ya shahara wajen haddasa ciwon hanta
 4. Zak aiya haduwa da farfadiya sanadiyyar hakan wato (seizure) in ka zamo addict
 5. Duk da AMPICLOX antibiotics ne akwai antibiotics din da ba ahadashi dashi ashaโ€ฆ shiyasa nafadamuku ko likita sai ya auna kafin rubutashi.
 6. Ko jira jirai da kananun yaran da akewa allurar rigakafin BCG ba a basu AMPICLOX a tsakaninโ€ฆ hantarsu na iya ta6uwa ko su hadu da zagwanyewar 6argo
 7. Ba’a hada shan AMPICLOX da Ja da yellow๐Ÿ’Š

Ampiclox ba’a hadashi da wadannan magungunan” (BCG vacine, cholera vaccine, demeclocycline, doxycycline, azithromycin, Allupurinol, minocycline, tetracycline, typhoid vaccine

 1. Yana iya bakinka ya rika kwailewa yana jini akai akai
 2. Yana iya lalata lafiyar aikin koda (kidney) da sauransu

Don haka ku hankalta, mutum ya kiyayi shan antibiotics daka bama sai AMPICLOX ba. Kai magani ma baki dayansa ka kiyayi shansa daka GUBA ne kaje wajen wanda yasan magani ya dubaka ya baka shawarar abunda ya dace.

Wani ciwon shawara kurum yake bukatar abaka basaika sha magani ba. Allah yasa mun fadaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button