LABARAI/NEWS

Illolin da aka yi amfani dasu a 2019 aka ɓata Atiku ga talakawan Najeriya:

Illolin da aka yi amfani dasu a 2019 aka ɓata Atiku ga talakawan Najeriya:
1- Ance zai sayar da NNPC.
Tsakaninmu da Allah miye amfaninta ga talakkan Najeriya?
2- Ance baida kishin addini.
Tsakaninmu da Allah wa’yanda suka sama yanzu amfanin mi sukayima addinin Musulunci?
3- Ance ɓarawo ne.
Tun 2019 Atiku yake adawa da gwamnati amma har yanzu ko da wasa bamu taɓa ganin an gayyace shi EFCC ba ko sau ɗaya ne.
4 Ance idan yahau Mulki France zata yi yadda takeso.
Tsakanin mu da Allah yanzu wane zaman lafiya ko kwanciyar hankali muke ciki?
5- Ance in Atiku yazama shugaban kasa bazai bari Universities na gwamnati su rayu ba saboda tashi University.
Tsakaninmu da Allah wane hali Jami’oin mu suke ciki?
Gaskiya kar mu ƙara bari kowa ya wautar da hankali da tunanin mu.
Kawai muyi Addu’a Allah yayimuna zaɓin abinda yafi Zama Alkhairi.

Dan Almajiri

©Adamu A Ahmad

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button