ylliX - Online Advertising Network INA DA JININ NAJERIYA A JIKINA - GIMBIYA MEGHAN - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

INA DA JININ NAJERIYA A JIKINA – GIMBIYA MEGHAN

INA DA JININ NAJERIYA A JIKINA – GIMBIYA MEGHAN

Sirikar sarki Chales na uku, Meghan Markle ta ce wani bincike da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa tana da nasaba da Najeriya ta wajen kakanni.

‘Uwar gidan Yarima Harry a wata hira ta musamman da ta yi da Spotify, ta ce binciken kwayoyin halitta da aka mata shekaru da suka gabata, an tabbatar mata da cewa tana da jinin Najeriya a jikinta da kusan kashi 43 cikin 100.

Sai dai ko da aka tambaye ta daga wacce kabila take a Najeriyar, ta ce bata da masaniya a kai, amma za ta fara bincikawa nan ba da jimawa ba.

A baya-bayan nan ne dai Gimbiya Meghan ta bayyana cewa tana da jinni biyu a jikinta, amma ba ta yi cikakken bayan kan asalin nata ba.

A shekarar 2015 ne Mujallar ELLE ta wallafa labarin Gimbiya Meghan game da asalinta na ruwa biyu.

A watan Satumba na 2019, Gimbiyar ta yi jawabi ga asalinta na launin fata a karon farko tun lokacin da ta auri Duke na Sussex. Ma’auratan sun zagaya zuwa wasu kasashen Afirka a wannan shekarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button