Videos

Ina son Adam a zango da Ali Nuhu su wayar dani inji wata yar Fulani

Ina son Adam a zango da Ali Nuhu su wayar dani inji wata yar Fulani

An samu wata budurwa yar jihar adamawa wacce tayi tattaki daga chan tazo har nan saboda asata a harkar film wanda kowa yasa nisan dake tsakanin jahar Adamawa da jihar Kano Amma wannan budurwa haka ta dauko hanya tazo saboda wannan burin nata ya cika

Yayin da tazo ta hadu da wani saurayi wanda shine yace zai hadata da wa’yannan jaruman biyu sai dai kuma babban rashin Sa’ar da akayi shine bai samu koda sisi ba a jikin wannan budurwa kuma a kalamansa ya nuna cewa gabashi kanta amma sam taki

Wannan budurwa ta burge mutane saboda yadda ta nuna cewa tana da kamun kai inda tace itafa a inda za’a samu matsala da ita shine ace za’a aikata wani abu wanda ba daidaiba to ita anan ne bata da kirki wanda kuma daman haka ake so mace ta gari ta kasance

Tace ita babban birninta shine taga Ali Nuhu da jarumi Adam a zango saboda tanaso su mayar da ita wayayyyiya ta zama yar birni itama ana mata kallo cikakkiyar wayayyiya wannan shine babban birninta a rayuwa

Tace ita koda wanke wanke akasata zatayi saboda bata da girman kuma tace koda kudi ne ake da buƙata mahaifinta bashi da matsala zai iya baya ko nawa ne amma sai yaga yadda abu ya kankama Allah ya hadata da wa’yannan jarumai da take nema

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button