ylliX - Online Advertising Network INEC ta yi gargaɗi kan tashe-tashen hankula gabanin zaɓen 2023 - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

INEC ta yi gargaɗi kan tashe-tashen hankula gabanin zaɓen 2023

INEC ta yi gargaɗi kan tashe-tashen hankula gabanin zaɓen 2023

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, Mahmood Yakubu ya ce yana fargaba game da ƙaruwar kai hare-hare yayin da ƙasar ke shirya wa babban zaɓen ƙasar a watan Fabrairu mai zuwa.

Ana dai fargaba game da yiwuwar samun tashin-tashina a zaɓen na baɗi wanda ake ganin zai yi zafi.

 

 

Yakubu ya ce hukumar zaɓen ta gano cewa an samu hare-hare 50 masu alaƙa da zaɓen a cikin watan farko na fara yaƙin neman zaɓe.

Shugaban na INEC ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da hukumar ta kira bayan kai wa ofisoshinta biyu farmaki.

A Najeriya dai gwamnati na ci gaba da yunƙurin ganin sun magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da na masu iƙirarin jihadi da kuma na ƴan bindiga masu garkuwa da mutane

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button