Innalillahi bom ya kashe Fulani 27 tare da jikkata Wasu a dajin Nasarawa

Innalillahi; wani bomb yayi sanadiyar rasuwar makiyaya da kuma Fulani ashirin da bakwai tare da jikkata Wasu da dama a jihar Nasarawa
Harin wanda aka tabbatar da cewa sojojin sama ne suka kai shi ya yi sanadiyar rasuwar Fulani ashirin da bakwai tare da jikkata Wasu da dama a cikin dajin jihar Nasarawa
Wannan hari dai ya biyo bayan da ake cigaba da sabon rikice rikicen tsakanin sojoji da kuma Fulani a cikin dajin lamarin da ya haifar da mummunan asara ga Fulani
Tuni dai miyati Allah watoh kungiyar Fulani ta nemi baasi kan wanna harin da Sojojin suka kai kan Fulani ,tare da jan hankali gomnati jihar kan wanna sara da suka tafka
rashin tsaro dai a kasa Nigeria na daya daga cikin manyan abubuwan da suke matukar samun kasar nan la’akari da yadda yan bindiga ke cigaba da ayyukan su a cikin daji
Wanna ya sanya wasu daga cikin manyan hanyoyi a kasar nan ke gagarar mutane biyo bayan yadda yan bindiga suka mayar da hanyoyin kamar gidan su tare da saka fargaba a zukatan al umma don gudun kar su kama su