LABARAI/NEWS

Innalillahi, Allah yayiwa Dr Ahmad BUK kano Rasuwa

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah yayiwa Shahararren malamin addinib Musulunci Rasuwa, wato Dr. Ahmad Buk wanda aka fi sani da bompa, muna rokon Allah yayi masa rahama ya gafarta masa zunubansa, yasa mu kuma mu cika da imani

DR. AHMAD BAMBA (BUK)
RAYUWA MAI TARIN ALBARKA

Allah ya karbi hidimar da kayi wa hadisan Manzon Allah S.A.W. Allah ya baka ladan ilmantar da al’umma. Tabbas an shuka alheri. Albarkar rayuwa ta bayyana. Sai dai addu’ar Allah ya karba. Ameen.

Jama’a mu tashi tsaye wajen tanadin guzurin wannan babbar tafiyar wacce ba dowowa. Yadda kake jin labarin rasuwar wasu su ma haka suka ji labarin rasuwar wasu kafin tazo kansu. Hakan ke tabbatar da cewa za ta zo kan kowa.

Allah Ka gafarta wa Mallam, Ka haskaka makwancinsa, Ka had’a shi da manzon rahama S.A.W cikin aminci. Mu kuma ka Kyautata qarshenmu. Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button