ylliX - Online Advertising Network Innalillahi Motoci sun murkushe masu tafiya a kasa uku har lahira a Anambra - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Innalillahi Motoci sun murkushe masu tafiya a kasa uku har lahira a Anambra

Innalillahi Motoci sun murkushe masu tafiya a kasa uku har lahira a Anambra

An murkushe mutane uku har lahira yayin da wani direban wata babbar mota kirar Scania ta kasuwanci mai lamba: LSD697YD da wani direban wata bas mai launin shudi/farar fata Mistibuchi L300 mai lamba: LEH596XA da ba a tantance ko wanene ba suka yi karo.

Mummunan hatsarin ya afku ne a kan gadar Onitsha ta hanyar Asaba zuwa Onitsha a ranar Juma’a.

An tattaro cewa mutane 10 da suka hada da maza shida manya da mata hudu ne suka shiga hatsarin. Yayin da mutane uku, maza biyu da mace daya suka mutu nan take, mata uku kuma suka jikkata.

A cewar wani ganau, wadanda lamarin ya rutsa da su, masu tafiya ne a kan gadar.

Tawagar masu aikin ceto na hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Onitsha, ta kai wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibiti, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar mutanen uku tare da ajiye gawarwakinsu a dakin ajiye gawa na asibitin.

Da take tabbatar da faruwar hatsarin a madadin kwamandan sashin, mukaddashin jami’ar ilimin jama’a ta FRSC a Anambra, Margaret Onabe, ta ce a halin yanzu wadanda suka jikkata na samun kulawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button