LABARAI/NEWS

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Ƴan ta’adda sun kashe jami’an tsaron NSCDC 7 a wajen hakar ma’adinai na Birnin Gwari

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Ƴan ta’adda sun kashe jami’an tsaron NSCDC 7 a wajen hakar ma’adinai na Birnin Gwari

 

Wasu da ake kyautata zaton yan fashin jeji ne sun kai hari kan jami’an hukumar tsaron farar hula, NSCDC inda su ka kashe bakwai daga cikinsu a wani wurin hakar ma’adinai a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna

 

 

 

Wata majiya ta shaida wa mana cewa yan bindigar sun rasa mamba guda daya a yayin wani artabu da bindiga a wurin hakar ma’adinai da wasu yan kasashen waje ke gudanar wa a karamar hukumar

 

A cewar majiyar tuni aka ajiye gawarwakin jami’an a asibitin kwararru na Barau Dikko da ke cikin babban birnin Kaduna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button