LABARAI/NEWS
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Ɓarawo yaji mummunan rauni bayan da ya Kade Mutane Hudu a Motar da ya sato

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Ɓarawo yaji mummunan rauni bayan da ya Kade Mutane Hudu a Motar da ya sato
An samu mummunar hatsarin ne a shataletalen Bahago dake Cikin garin Minna a jihar Niger da rana Lokacin da wata mota kirar camry ta Kwace hannun wani Barawo
wanda aka biyo a guje bayan daya sato motar daga kasuwar kure dake Babban Birnin Jihar Nejan sai dai an sami matsala ba’a ankara ba ya buge wasu mutane hudu
Yanzun dai haka wasu Mata biyu mabarata da Wani mai mashin dauke da wanda ya goyo an garzaya dasu asibiti
Tuni dai wanda ake zargin ya shiga hannun Jami’an tsaro tun ranar asabar bayan da Shima ya samu mummunar rauni