LABARAI/NEWS

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Iyayen ɗaliban makarantar Yauri da aka sace sun fara yin karo-karo don kuɓutar da ƴaƴansu

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Iyayen ɗaliban makarantar Yauri da aka sace sun fara yin karo-karo don kuɓutar da ƴaƴansu

 

Iyayen sauran ɗalibai 11 da a ka yi garkuwa da su a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke garin Yauri a Jihar Kebbi sun fara shiri na tara kudin fansa Naira miliyan 100 domin a sako ƴaƴansu

 

a ranar 17 ga watan Yuni 2021 aka sace dalibai sama da 80 a lokacin da wasu yan bindiga karkashin jagorancin wani ƙasurgumin ɗan fashin jeji Dogo Gide suka kai hari makarantar

 

 

Daga baya an sako yawancin daliban ga gwamnatin jihar bayan an biya kudin fansa

 

Sai dai bayan watanni 19 ‘yan ta’addan na ci gaba da tsare 11 daga cikin daliban inda suke neman kudin fansa Naira miliyan 100

 

iyayen daliban da aka sace da suka hadu a harabar makarantar sun koka kan yadda suka yanke shawarar daukar al’amura a hannunsu bayan gwamnati ta gaza musu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button