ylliX - Online Advertising Network INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJIUN !!! - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJIUN !!!

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJIUN !!!

Yan uwa kuzo mu hadu a taimakawa wannan baiwar Allah me suna Sadiya ‘yar cikin garin Kano, ta yi aure a wajen kano tana da yara huɗu.

Lokaci guda in aka kira wayarta ba a samu in an kira mijinta sai yace ba ta kusa ko ta yi barci sai dai ya bawa ‘ya’yanta su gaisa da yan uwan nata.

 

 

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ashe ya kulle Sadiya a ɗaki yana azabtar da ita ba ya ba ta abinci, ruwa rabin kofi yake bata a wuni sai kunu rabin kofi Sai Hazbiya da kullum yake gasa mata ya bata.

Ya hana kowa danginsa zuwa gidanta kwatsam mahaifiyarta ta kira tana son magana da ita, kamar kullum yace Sadiya ta yi barci, mahaifiyarta hankalinta ya kasa kwanciya ta nufi garin da Sadiya take aure zuwanta ke da wuya ta ga mawuyachin halin da ‘yarta take chiki.

Babu abinda Sadiya ta iya furtawa sai “Dan Allah ki tafi dani mugune”😭😭😭 sadiya tana cikin yanayi, a kula da ita da lafiyarta.

Yanzu haka tana kwance a asibitin Malam Aminu kano dake nan kano, dan Allah wanda Allah ya bawa dama da iko dan Allah ku taimakawa Sadeeya gashi abin har kwakwalwarta ake tinanin ya taɓa,

Za’a mata hoton kwakwalwa dan Allah, wanda Allah ya bawa iko ya taimaka mata sadaka ba ta kadan ba ta yawa, Mahaifinta Allah ya masa rasuwa, dan Allah mu hadu mu taimakawa yar uwarmu.

Domin karin bayani za a iya tuntubar wannan number 081237416048.
Ga Wanda Allah yabashi iko zai’iya Taimakawa Ta Wannan Asusun.

Bank: GT Bank.
Acc no: 0528884169.
Acc name: Mims Multi Synergy Foundation.

Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi,ka bada a duniya ka tsinta a mizani ranar gobe kiyama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button