Videos

Innalillahi wa’inna’ilaihi raji’un ; chanzin kudi ya fusata mutane

Wasu daga cikin mutane kasa Nigeria na cigaba da nuna rashin jin dadin su kan deba karbar tsohon kudi a fadin kasar nan lamarin da ya ke cigaba da haifar da matsaloli da dama

 

 

Al umma dai na cigaba da nuna rashin jin dadin su kan wa’adin lokacin da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina karbar tsohon kudin Naira wanda ya haɗar da dari biyu ,dari biyar da dubu daya

 

 

Chanzin kudin dai ya janyo cece kuce manya da kanana a fadin kasar nan duba da yadda Al umma ke cigaba da nuna rashin jin dadi ƙarara

 

 

 

 

Duk da cewa majalisar ƙasa ta tarayya da kuma ta wakilai na cigaba da yin kokarin su kan ganin an shawo kan gomnan babban bankin kasa CBN emefele don ganin ya kara wa’adin lokacin daina karbar kudin

 

 

Sai dai kuma shugaban kuma gomnan babban bankin kasa CBN din ya fito ya sake jaddada wa yan kasa kan cewa babu gudu babu ja da baya kan wa’adin daina karbar kudin

 

 

Wannan abu dai na cigaba da haifar da cece kauce a fadin kasar lamarin da ya sanya ake kallon hakan ka iya taba gomnatin su musamman jam’iyyar APC

 

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button