Innalillahi wa’inna’ilaihi raji’un ; yadda Al umma ke shan wahala wajen saka kudi a banki na daukar hankali

Al umma na cigaba da kokawa kan rashin yawaitar sababbin kudi a hannun su tun bayan da aka ayyana ranar talatin da daya ga watan Janairu a matsayin lokacin dai amfani da tsofaffin kudin na Naira
Al umma a jihar Kano dama sauran sassan kasar nan na cigaba da kokawa hadi da rashin jin dadi yadda babban bankin kasa CBN yaki amincewa ya kara lokacin daina karbar tsofaffin kudin takarda ta Naira
A ranar talatin da wata Janairu dai shine lokacin da babban bankin kasa ya ayyana a matsayin lokacin daina karbar tsohon kudi lamarin da ke cigaba da haifar da matsaloli da dama a fadin kasa
Masu tsofaffin kudin a hannun su sun shaida mana yadda suke matukar shan wahala wajen saka kudin nasu a banki gabanin lokacin da za’a daina karbar kudin nata karatowa
Mutane da dama sai tuni suka daina karbar tsohon kudin na Naira sakamakon tsoro da fargaban yin asara tun kafin lokacin da babban bankin na kasa ya bayar la’akari da yadda suke matukar shan wahala lokacin da suka je banki domin saka kudin nasu