innalillahi Wani mutum ya rasu a gurin bin layin cire kudi a banki

Innalillahi wani labarin mara daɗi da muke samu shine yadda wani bawan Allah ya rasa ransa a gurin bin layin cire kudi a banki lamarin da ya sanya mutane cikin fargaba
Mutumin wanda ba’a san ko waye ba ya yanke jiki ya fadi wanda tuni rai yayi halin sa a gurin cire kudi a banki first bank inda mutane suka shiga cikin rudani matuka
Mutumin wanda ya zo cirar kudi sai dai kuma ganin yadda Al umma sukayi matukar yawa a gaban sa kafin a zo kan sa mutum ya yanke jiki ya fadi
Tun bayan sauya kudin Nigeria ka akayi al umma da dama ba cigaba da kira ga gomnatin kan ta duba hali da mutane suka shiga na kunci da rashin kuɗi a hannun su
Chanzin kudin dai ya matukar janyo koma baya a wasu abubuwa da dama a fadin kasar nan musamman byadda mutane ke neman kudin da zasu kashe a gidajen su wato cash