Videos

Innanillahi Yanzu yanzu uwa da danta sun saki video akan wadda tace matan Niger karuwai

Innanillahi Yanzu yanzu uwa da danta sun saki video akan wadda tace matan Niger karuwai

A cigaba da fada tsananin matan Niger da kuma matan Nigeria abi kullum ya kara dawowa danye wanda akaji wata mata ita da danta sun kara sakin martani ga yan Nigeria wanda da ake tunanin komai ya fara zuwa karshe amma kuma wannan matar zata dawo da hannun agogo baya wanda ta cigaba da zagi dacin mutunci

Inda a yanzu ma haka Tiktok ta kara hargitsewa wanda ake ganin wannan rigimar zata iya kaisu har kotu tunda an kasa samun daidaito da kuma fahimtar juna duk da kasashen biyu suka makwabtaka da juna amma wasu dalilai sunsa za’a samu sabani

Bayan wannan matar da tayi abin ta fito fili ta bayar da hakuri amma duk da haka kallon abun ake a matsayin rigamar da take dawowa danya a koda yaushe

Duk da hukumar yan sanda sun shiga wannan rigimar Amma mutanen kasar Niger sun kasa sanyawa zuciyarsu ruwan sanyi kullum kara ballo ruwa suke akan wannan rigimar

An jiyota ita da danta suna fadar bakaken maganganu zagi ta uwa ta uba wanda aka bayyana hakan a matsayin cin fuska da kuma rashin kirki da rashin tarbiya mu dai fatanmu shine Allah ya tsayar da wannan rigimar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button