LABARAI/NEWS

IPOB ta hana rera taken Najeriya da cin naman shanu a yankin Igbo

IPOB ta hana rera taken Najeriya da cin naman shanu a yankin Igbo

Kungiyar da ke fafutukar ɓallewa daga Najeriya da son kafa Jamhuriyar Biafra wato IPOB, ta haramta yin taken Najeriya da cin naman shanu a wuraren bukukuwa da daukacin makarantun da ke Kudu maso gabashin kasar.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun kakakin ƙungiyar Chika Edoziem.

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta fitar da sabbin dokoki bakwai da ta ce na sabuwar shekara ne da za ta fara amfani da su a 2022 ɗin.

Ga dai saƙon nata kamar yadda yake a sanarwar:

. Saƙon farko ya ce a 2022 ƙungiyar za ta ci gaba da fafutukar ganin an saki jagoranta Nnamdi Kanu, wanda suka kira “fursunan da ake tsare da shi ba tare da ya yi laifi ba.” Ƙungiyar ta ce za ta kira fafutukar da taken “Kamfe don neman sakin fursunan da ake tsare da shi ba tare da ya yi laifi ba.”

A sakamakon wannan kamfe, ƙungiyar ta buƙaci dukkan mambobinta da al’ummar yankin da ta kira Biafra da su sauya hotunan da ke kan shafukansu na sada zumunta ta hanyar sanya fastar kamfe ɗin.

2. Saƙo na biyu shi ne wanda ƙungiyar ta umarci mambobin IPOB a ko ina a faɗin duniya da su gaya wa iyalansu wannan umarnin. “Za mu fara zanga-zanga a fadin duniya a manyan birane.

“Za mu yi zanga-zangar ce a ofisoshin jakadancin Birtaniya da Majalisar Dokokin Birtaniya da gidan Firaministan Birtaniya da ofisoshin jakadancin Kenya da na Najeriya da manyan ƙungiyoyin ƙasashen waje kamar su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da Amnesty International da kuma kafafen yaɗa labarai,” a cewar sanarwar.

3. Abu na uku a jerin saƙonnin shi ne IPOB ta ce za ta ƙirƙiri wani sabon sashe da zai yi aiki a ƙarƙashin ƙungiyar. Ta ce za a ayyana sashen a matsayin Sashen Ilimi na IPOB.

“Babban aikin sashen shi ne koyar da tarihinmu da harshe da kuma al’adarmu ga ƴaƴanmu.

“Muna da littattafai uku da za mu wallafa a wannan shekarar nan don cimma hakan. Sannan bayan bayyana su ga al’umma, za a kira marubuta ‘ƴan yankin Biafra’ da kuma wallafa littattafai na ƴan firamare da sakandare.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button