Fadakarwa

ISTIBRA’I

ISTIBRA’I

Wannan wani hukunci ne na lallai ga duk Macen da ta sami saduwa da namijin da ba mijinta ba, walau me aure ko mara aure duk hukuncin ya hau kansu.

Malamai sun ce wajibi ne ta jira har sai tai haila sau 1 kafin ɗaura aure in tsakanin saurayi da budurwa ne, ko kuma kafin komawa shimfidar mijinta idan Matar aure ce, Wanda hakan shine zai barrantar da ita cewa babu ɗa ko ciki daga abinda ya faru tsakaninta da wani.

Matar auren da tai zina aurenta na nan saide bazata bari mijinta ya sadu da ita ba har sai tai jini ɗaya (haila) kamar yadda nace. Dole kiba mijinki dukkan uzurin da zaki iya basa na ƙarya don ganin kin yi jini kafin ya qara kusantarki.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Toh anan ne bisa wancan hukuncin na “istibra’i” idan na haɗasa da ilimin kimiyya zaku fahimci irin yadda addinin musulunci ya amsa sunansa na wayayyen addini.

Domin Idan Mace nada ciki tabbas bata Haila, don haka abinda musulunci ke gujewa shine; ta yiwu sanda Mace tai zinar a kwanakin ovulation ko gab da ovulation ta ke, don haka tana iya daukar cikin wani kai tsaye alhalin me aure ce!

Shiyasa Manzon Allah (SAW) ke cewa: “Duk wanda yai imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” Abu-dawud : 1847.

Ruwansa anan na nufin kar yaje ya zuba maniyyinsa jikin matar da batasa ba muddin yai imani da Allah.

Domin idan fa akai dace a kwanakin ovulation tai zinar tohfa tana iya samun cikin Mazaje biyu mabam-banta lokaci guda. Kwarai! Mace na iya samun cikin yara ƴan biyu wato (twins) amma kowanne ubansa daban, abinda ake kira (Superfecundation) kamar yadda a hotunan ƙasa zaku gani.

A hotunan kasa zakuga yara ne ƴan biyu, lokaci guda aka haifesu, duk uwarsu ɗaya, amma kowanne kalarsa daban…
Wanda hakan ya faru ne sakamakon kwanciya da uwar tai da mutum biyu ko samari biyu mabanbanta mijinta da kuma wani can acikin kwanakin ovulation da galibi basa wuce yini uku.

Kunga ɗaya bature ne, ɗaya ɓakar fata, mu hakan na iya wahalar fahimta a zahira tunda dukkanin mu bakaken fata ne. Shyasa dole sai an sanya tsoron Allah.

Haka nan akwai ɗaya yanayin da mutum biyu Mazan kan zamto sun haifi mutum guda ma’ana kowa da ƙwan halittarsa jikin yaron wato “Chimera”

Ko kuma ma de kije ki ɗau cikin Mutumin da ba mijinki ba, ba lalle sai anga twins ba.
.
Don haka anan zamu fahimci hikimar musulunci.

Shiyasa wani a haifa masa ɗa kaga sam ko kusa bai halin ubansa ba, kai ko wani na gidan zakaga bai biyo ba a halaye, watakil ashe ha’intar uban akai, wani yazo ya haifa ma ɗa kanata dawainiyarsa data karatunsa, kana zaton naka ne, karshe ka mutu har ya ci gadonka kuma ita Macen tasan komi galibi, amma tai shiru saboda rashin tsoron Allah.

Shiyasa yanzu akwai paternity test ga duk me kokonto ana iyayi agano mahaifin yaro koda kuwa cikin Maza dubu ne’ is 100% accurate.

Don haka samari ma da ƴan Mata a kiyaye wannan hukuncin da yawa bakwa istibra’i ake zuwa a daura aure, gashi abin kullum kara kazanta yake.

Allah (SWT) ya tsaremu, ya tsare mana imanin mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button