LABARAI/NEWS

SHUGABANNIN KUNGIYAR IZALAH SUN ZIYARCI GWAMNAN KEBBI

SHUGABANNIN KUNGIYAR IZALAH SUN ZIYARCI GWAMNAN KEBBI

 

Wakilan Izalah bisa jagorancin Shugaban kungiyar Jibwis Nigeria na kasa Imam Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, sun ziyarci gwamna Kebbi Sen, Abubakar Atiku Bagudu, a fadar gidan Gwamnati dake Birnin Kebbi.

 

A cewar jagoran tawagar (Shugaba Imam Bala lau), sun je gidan gwamnati ne domin nuna godiya ga gwamnan kan samun zaman lafiya da ci gaban jihar tare da godewa gwamnan bisa samun tallafin Naira Miliyan Hamsin (N50,000,000.00) na tallafin da Gwamnatinsa ta basuwa domin gina Jami’ar As-Salam Global University Hadejia a jihar Jigawa.

 

Bugu da kari, ya sanar da Gwamnan jihar kan yadda aka warware rikicin da ke faruwa a cikin shugabannin kungiyar na jihar Kebbi tare da gabatar da sabbin shugabannin jihar.

 

A lokacin da yake mayar da nashi jawabin, Mai Girma Gwamna Sen, Abubakar Atiku Bagudu, yayi godiya ga Shugabannin a ziyarar da suka kawo masa da Kuma yabawa Kungiyar ta JIBWIS na gudunmawa da kokarin da suke basuwa ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, GCFR da kuma jiharsa (ta Kebbi). Gwamnan ya kara godiya ga wakilan akan addua’arsu da goyon bayan da suke basuwa. Kuma ya gabatar musu da yara guda 30 da Malami Daya Wadanda aka karbo na FGC Yauri ya nemi da suyi musu addu’a.

 

Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jagoranci Sheikh Bala Lau da sauran shugabannin Izala zuwa dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati inda suka gudanar da addu’o’i na musamman ga daliban da aka sako da kuma malamin kwalejin gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri.

 

Shugaba Bala lau bayan sun kammala ganawa da Daliban da da Malami Daya, da yi musu addu’a, ya yabawa Gwamnatin Jihar Kebbi (Kebbi State Government of Nigeria) na kokarin kubutar da wadannan Daliban.

 

Shugaba Sheikh Bala lau, yayi matukar godiya da yabo ga Gwamna Sen, Abubakar Atiku Bagudu, cewa ya cika alkawalin da ya dauka na bada tallafin Miliyan Hamsin, ga Jami’ar As-Salam Global University Hadejia. A ranar da aka kaddamar da ita.

 

Shugaban Izala ya bayar da shawarar gudanar da taron tuntubar juna tsakanin Gwamnoni da malaman addini a lokaci-lokaci domin tuntuba tare da lalubo hanyoyin magance kalubalen da ake fuskanta da suka shafi tsaro, tattalin arziki, shugabanci da siyasa.

 

Daga cikin Tawagar akwai Sakataren Izalah na kasa Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Ya gabatar da takardar yabawa da godiya daga Shugaban kungiyar Jibwis Nigeria Sheikh Abdullahi Bala lau zuwa ga Gwamna Sen, Abubakar Atiku Bagudu.

 

Daga cikin Tawagar Shugaba Bala lau akwai:

Sheikh Abubakar Giro Argungu

Sheikh Alaramma Ahmad Suleiman Ibrahim Kano da Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo sauransu.

 

Signed,

Yahaya Sarki

Special Adviser (SA) Media

to Kebbi State Governor

  1. 9th January, 2022

 

Fassarar: Munir Assalafiy

Related Articles

One Comment

  1. Thanks for another excellent post. Where else could anybody get that type of info in such an ideal way of writing? I have a presentation next week, and I am on the look for such information.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button