ylliX - Online Advertising Network JAGORAN IPOB ZAI SHA KUDI DAGA GWAMNATI NNAMDI KANU - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

JAGORAN IPOB ZAI SHA KUDI DAGA GWAMNATI NNAMDI KANU

JAGORAN IPOB ZAI SHA KUDI DAGA GWAMNATI

Yau Laraba Babbar kotun tarayya da ke da zama a Umuahia babban birnin jihar Abia ta bukaci gwamnatin Nigeria ta biya shugaban kungiyar ‘yan aware na IPOB Nnamdi Kanu Naira miliyan 500 a matsayin diyya

Mai shari’a Evelyn Anyadike ce ta yanke hukuncin a zaman kotun na yau kan shari’ar da Kanu ya shigar a kan cewar an tilasta dauko shi daga kasar Kenya zuwa Nigeria a watan Yunin 2021, inda ya ce hakan ya saba ka’ida.

Makonni biyu da suka wuce, kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da Gwamnatin Nigeria take yi wa madugun ‘yan awaren, Nnamdi Kanu a wata shari’ar ta daban da aka yi.

Hakika Nnamdi Kanu dan gata ne, da suka tashi kaishi kara Kotu sai suka kaishi gurin Alkalan da suke kabila daya dashi, wato gurin Alkalai ‘yan uwansa, dole su taimakeshi su kubutar dashi duk da ta’adin da ya yiwa Kasa

A dayan bangare, bayan da shugaban NDLEA Buba Marwa ya amince a yiwa Abba Kyari sharri da batanci, da suka tashi kaishi Kotu sai suka kaishi Kotun da Alkalin dan kabilar IPOB ne a daidai lokacin da Abba Kyari ya yaki manyan Kwamandojin yakin IPOB da suka taso zasu wargaza Nigeria

Nnamdi Kanu gashi yana shirin samun ‘yanci duk da abinda ya aikata na cin amanar Kasa, kuma Kotu ta bukaci Gwamnati ta biyashi har da diyya na Kudi Naira Miliyan dari biyar, to ai shikenan tunda yana da gata da masu daure masa gindi akan abinda yake yi

Allah Ka kubutar mana da jarumi DCP Abba Kyari, Ka tabbatar masa da nasara akan sharrin NDLEA maciya amanar Kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button