LABARAI/NEWS

JAMI’AN TSARO SUN KAMA MOTA DAUKE DA BAMA-BAMAI A JIHAR KANO

JAMI’AN TSARO SUN KAMA MOTA DAUKE DA BAMA-BAMAI A JIHAR KANO

Rundunar ‘yan sanda a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu bama-bamai a cikin wata mota kirar Mercedes Benz da ke kan hanyar Chiranchi a unguwar Dorayi a jihar Kano

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin makamai da alburusai da aka kwato tare da gabatar da ‘yan ta’adda tare da aka kama da laifuka daban-daban a jihar

CP Dikko ya ce mutanensa da ke aikin bincike ne suka tare motar domin bincike yayin da suka kan aikin binciken wadanda ke cikin motar suka bude wuta kana suka tsere

A cewar sa Tawagar yan sanda karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef a yayin da jami’an leken asiri da ke sintiri a unguwar Chiranchi Dorayi Kano, a yayin gudanar da bincike sun kama wata mota kirar Mercedes Benz

Yayin da suke shirin tsayarwa da binciken motar sai mutanen da ke cikinta suka bude wa ‘yan sandan wuta inda jami’an ‘yan sandan suka yi artabu da yan bindigar da suka gudu suka bar motar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button