Videos

Jarumi Daddy Hikima ( Abale) zai fito takara

Jarumi Daddy Hikima ( Abale) zai fito takara

Matashin jarumin kannywood wanda tauraruwarsa take haskawa wanda ake ganin a yanzu duk cikin jarumai maza babu wani wanda ya kaisa taka rawar gani kuma yake yin abubuwa wanda na kowa yake yiba sai shi

An bayyana cewa jarumin yanzu ya zama cikakken dan siyasa kuma yana yunkurin fitowa takara acikin wata sabuwar jam’iyya wanda ke ganin gaskiya wannan matashin bai taki zaman lafiya domin yanzu su kansu yan siyasar abin yafi karfin sai masu mugun kudi acikinasu

Jarumin yace yana fatan mutane zasu zabe shi domin yana da kyawawan manufofi akan wannan takarar tasa ya shirya domin kawowa al’umma cigaba da zaman lafiya

Wannan dai maganar takarar tashi tana nuna cewa lallai yanda matukar basira da kuma kishin al’umma domin ba kowane yake da wannan zuciya da kuma kishin son cigaban al’umma ba amma shi yayi wannan tunanin hakika mutane sun yaba masa kuma ana masa fatan alkhairi

Sai dai kash babban abinda zai bashi matsala shin jarumin bashi da cikakken kudin dazai jawo hankalin mutane harsu zabeshi tunda yanzu abin ya koma komai sai da kudi mudai a matsayinmu na masu kishin al’umma Muna fatan duk wanda zai kawo cigaba acikin al’umma Allah ya zaba mana shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button