Jerin Yan kannywood da suka rasu a 2022 da kuma cututtukan da suka yi silar Rasuwar su

Jerin Yan kannywood da suka rasu a 2022 da kuma cututtukan da suka yi silar Rasuwar su
NURA MUSTAPHA WAYE
Nura ya rasu ne a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya an kuma yi jana’izarsa da misalin karfe 11 na safen 3 ga watan july 2022
Nura Mustapha darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana’antar ta Kannywood.
Fim din Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya
Kiyasi da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa fim din shi ne ya fi yawan masu kallo a dandalin YouTube da ake nuna fim din
A daren ranar da zai rasu Makusantansa sunce sun rabu da shi lafiya a daren jiya amma kamin wayewar gari sai aka tadda gawarsa amma ba’a san silar rasuwar tasa ba har yanzu