NEWS

Jihar Lagos na cigaba da fuskantar barazanar nutsewa a ruwa

Jihar Lagos na cigaba da fuskantar barazanar nutewa a ruwa biyo bayan yadda ruwan da ya zagaje duniya yake cigaba da ambaliya

Ruwan dai a wannan damuna yana cigaba da tunbatsa biyo bayan yadda akayi ruwa kamar da bakin kwarya a wannan shekarar

Jihar ta Lagos dai ba daya daga cikin jihohin da masana suka tabbatar da cewa na cikin wani Hali sakamakon samun wani rahotoh na wani bincike na samun ambaliyar ruwa daga ruwan da ya zagaye duniya

Baya ga jihar ta lagosa jihohin da suka Hadar da jihar jigawa , Benue na daga cikin jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa wannan shekara inda manoma suka tafka babbar asara ta kimanin kudi miliyoyi

Wannan ambaliya da masana suka fada wadda ka iya afkuwa a jihar ta legas ta Sanya gomnatin jihar ta Lagos Bada umarnin gaggawa ga Al ummar da suke zama a bakin ruwa dasu tashi daga Nan Kuma da gaggawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button