Fadakarwa

JIN DADIN ZAMAN AURE

JIN DADIN ZAMAN AURE

MA AURATA.

Ba za ka taba jin dadin zaman aure ba har sai ka
fahimci wadannan abubuwan :-

➤ zaman aure ibada ne, ibada kuma tana tare da
barazanar samun cikas daga shedan.

➤ abokin zamanka ba mala`ika ba ne, ba kuma 100% ba ne, don haka zai iya yin kuskure.

➤ rayuwar aure zo mu zauna ce, zo mu bata, sbd hk ba kullum ne za a sha zuma ba.

➤ rayuwar aure tana bukatar hakuri, juriya da yi wa juna afuwa.

➤ abokin zamanka yana matukar bukatar ka, kai ma kuma haka.

➤ abokin zamanka yana da halaye biyu, mai kyau da mara kyau, idan ya yi maka mara kyau din, ka hararo bagaren mai kyau din nasa, yin hakan na iya sanyaya maka rai, ya kuma rage maka radadin damuwarka.

➤ babu yadda za ka yi ka samu abinda kake buri a zaman aurenka 100%, domin kuwa a duniya kake rayuwa, ba a aljannah ba.

➤ duk halin rashin jin dadin rayuwar aure da kake da abokin zamanka, akwai wadanda nasu ya fi naku muni, don haka sai ka gode wa Allah da ya bar taku iya yadda kuke.

➤ zaman aure yana bukatar sirri, sbd hk ka takaita baiyana matsalolin gidanka, ko da ga waliyyenka.
– a cikin makusantanka ba za ka rasa makiyin boye ba, da mai yi maka hassada, sbd hk baiyana matsalolin gidanka na iya faranta musu, sai ka yi hattara da masu ba ka shawara.

✎ zaman lafiyar rayuwar aurenka tana bukatar agajidaga wajen Allah, sbd hk ka rika saka shi a cikin adduoinka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button