Girki Adon UwargidaIslamic ChemistLABARAI/NEWS

JINKIRIN AURE, JARRABA NE DAGA ALLAH!

JINKIRIN AURE, JARRABA NE DAGA ALLAH!

Komai kusancinka da alakarka da MACE, kar ka tambayeta:

• Yaushe za ki yi aure?
• Ba ki yi aure ba har yanzu?

Irin wadannan tambayoyin, akwai wadanda saboda da takaici da ciwo, har KUKA suke in sun shiga daki. Kai ba zaka gane irin radadin da suke ji a ransu ba.

Kamar kai ne ka gamu da jarrabawar SPILLOVER a jami’a, shekaru 2 kana zuwa gyara; wani ya tambayeka cewa, “ME YA SA HAR YANZU BAKA YI GRADUATION BA?”

AURE a karan-kansa, ba kan kowa ya wajaba ba, matukar ba zaka afkawa alfasha ba. Akwai wadanda aure ya zame musu wajibi, wasu mustababbi (abin so), wasu makruhi, wasu ma haramun ne a kansu su yi auren. Wannan ka’idar tana hawa kan kowanne jinsi, ‘namiji’ ko ‘mace’ [Fiqh Al-Sunnah, 2/15].

AURE BABBAR NASARA CE A RAYUWA, MUSAMMA GA ‘YA MACE. Amma babu inda addini ya ce, in mace ba ta yi aure ba, ta zama ‘wata mai laifi’ ko in ta mutu bata yi aure ba zata shiga ‘Aljanna’ ba. Ba laifi ba ne ina mace ta zauna ba aure, matukar zata kiyaye mutuncinta.

A al’adarmu ake ganin, in mace bata yi aure ba, tamkar wani LAIFI ta aikita, ko a cikin gidaje, a gaban iyayenta, a yi ta tsangwama mata, kullum a cikin takaici.

✍️ Aliyu M. Ahmad
4th Shawwal, 1443AH
5th May, 2022CE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button