LABARAI/NEWS

JOSE MUJICA: Shugaban Kasa Mafi Talauci A Duniya

JOSE MUJICA: Shugaban Kasa Mafi Talauci A Duniya

Jose Mujica shugaban ƙasar Uruguay, shine shugaban ƙasa mafi talauci a cikin jerin shugabanin ƙasashen duniya.

 

 

Ya mulki ƙasar daga ranar 1 ga watan March 2010 zuwa 1 ga watan March 2015, yana amfani da kaso 90 cikin 100 na albashinsa na wata-wata dala dubu 12 wajen taimakawa mutane marasa galihu.

Sanda Jose Mujica yake kan mulki yana amfani da tsohuwar motarsa ƙirar Volkswagen samfurin Beetle wacce ya siya tun shekarar 1987, kuma shine yake tuƙa kansa da kansa.

Kuma har ya gama mulki ita kenan motarsa, kana ya mallaki gidan gona guda ɗaya ne tak kuma shi ma ba na a zo a gani ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button