ylliX - Online Advertising Network Kada ku dauki yajin aiki a matsayin tsani na biyan bukatun ku ~ Buhari ga ASUU - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Kada ku dauki yajin aiki a matsayin tsani na biyan bukatun ku ~ Buhari ga ASUU

Kada ku dauki yajin aiki a matsayin tsani na biyan bukatun ku ~ Buhari ga ASUU

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya sake yin kira ga kungiyoyin kwadago musamman kungiyar malaman jami’o’i da su guji yajin aiki a matsayin makamin biyan bukatunsu.

Ya yi wannan roko ne a jiya Alhamis a wajen bukin ranar Foundation/Convocation na Jami’ar Ibadan karo na 74 a cibiyar taron kasa da kasa, a Ibadan.

 

 

Buhari ya ce yajin aikin zai kara dagula halin da fannin ilimi ke ciki a yanzu tare da bata sunan jami’o’in gwamnati da ma kasa baki daya.

Shugaban wanda Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa Farfesa Abubakar Rasheed ya isar da sakonsa, ya kara yin kira ga kungiyoyin da su kasance masu kamun kai a kodayaushe.

Ya ce, “Abin takaici ne yadda a cikin shekara mai kamawa, kusan dukkanin kungiyoyin kwadago na jami’o’i, ASUU, SSANU, NASU, da NAAT, sun bayyana takaddamar kasuwanci da ta dade tana haifar da mummunar illa ga tattalin arzikinmu, wanda ba ya bukatar kalandar karatunmu sakamakon takaici da rashin tsaro a tsakanin matasan mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button