LABARAI/NEWS

Kadan Daga Cikin Bayanin da shugaban Kasa muhammadu buhari yayi a zantawar da yayi da Tambarin Hausa television

Kadan Daga Cikin Bayanin da shugaban Kasa muhammadu buhari yayi a zantawar da yayi da Tambarin Hausa television.

“Ina bin kudin tsarin mulkin kasar nan Kuma Ina aiki akan abunda nake da hurumi, Sannan Ina baiwa Hukumomin Gwamnatin tarayya Damar Gudanar da ayyukansu.

” Idan Yan Nigeria Suna da korafi Game da Wani jami’in Gwamnati Suna iya Sanar damu Domin daukar matakin da yakamata akansa ko wanene.

“Maganar aikin wutar manbila kuwa Muna Gudanar da Bincike Akai saboda akwai tsohuwar ministar Mai Mai Suna dezieni Alison madueke wadda yanzu haka tana London Kuma mun sayar da wasu kaddarorinta mun sakasu a lalitar Gwamnati.

Maganar noma kuwa Idan bakayi noma ba to yunwa zata kasheka kuwa, saboda mu. Rufe iyakokin Kasar nan Kuma mungs alfanun Hakan.

Babu Wanda yaci kudin Gwamnati da muka kyaleshi Kuma zamu Cigaba da Sanya idanu akan jami’an Gwamnati.

Babu shakka shugaban Babban Bankin Kasa na CBN ya Sanar Dani maganar sauya fasalin kudin Kasar nan Kuma na Gamsu da tsarinsa shiyasa na goyi bayansa..

Maganar tsaro a yankin arewa maso yamma masiface Kuma annobar Ce, saboda addini Daya, kabila Daya, yare Daya, Amma Suna kashe junansu Wannan Babbar masifa Ce Kuma Muna aiki Wajen kare Rayuka da dukiyrar al’umma.

Maganar zabe Mai zuwa kuwa duk Wanda yaci shi za’abaiwa Babu magudi saboda munyi abunda ya kamata.

akarshe nayi abunda zanyi Kuma kwalliya ta Biya kudin sabulu a ganina acewar shugaban Kasa muhammadu buhari yayin zantawar Sa da Tambarin Hausa television afadarsa Dake Birnin tarayya Abuja

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button