Videos

Kai tsaye daga wajen shagalin bikin mawaki Aliyu Nata jarumin kannywood

Kai tsaye daga wajen shagalin bikin mawaki Aliyu Nata jarumin kannywood

Mawakin wanda ya samu ya angonce a kwanan nan bikin nasa yayi armashi sosai kuma yasamu halartar manya mutane da kuma manyan yan kannywood mata da maza bikin masa ya shiga sahun manyan bukukuwan da baza a taba mantawa dasu wanda bikine daya bawa Kowa sha’awa

Kowa yasan mawakin yadda yake matukar kaunar aure yau kuma gashi Allah ya nufa ya samu ya angonce wanda kowa yana masa farin ciki da kasancewar sa ango

Tun wata tsohuwar waka da yayi wacce yake cewa Aure martaba dadi wanda wannan wakar itace wacce ta fito da mawakin har aka sanshi a ko ina musamman gidan Radio wanda sune suka dinga saka wakar har mawakin ya karbi a zukatan al’umma

Anga manyan jarumai da kuma manyan mawakan kanmywood a wajen bikin wanda sune sukasa bikin yayi armashi kuma kara sukayi masa tunda shima mawakin badaga nan indai wajen zuwa wajen bukine

Hotunan da akayi a wajen wannan bikin sun dauki hankalin mutane yan gari wanda aka dinga yi masa fatan alheri da kuma addu’ar Allah yabada zaman lafiya da zuri’a dayyiba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button