Kalli yadda mata sukayiwa Hamisu breaker a gidan biki

Kalli yadda mata sukayiwa Hamisu breaker a gidan biki
Wannan shine farin jini daga Allah hakika indai Allah yana sonka zaka dinga ganin soyayya daga wajen mutane har wa’yanda naka tsammani duk zasu dinga nuna maka soyayya wanda kuma Allah ne kawai yake ƙaddara hakan
Yayin da mawaki hamisu breaker yaje wani gidan biki yaga soyayya wacce bai taba fiskantaba daga wajen mutane da dama musammanma dai mata wanda daman yafi tarin masoya acikin yan mata
Babu wata mace wacce zatace batasan mawaki hamidu breaker ba saaboda yadda yake nishadantar dasu da wakoki masu dadi wanda har mutuwar aure anyi akan wata wakarsa
Anga manyan mata sun taso kamar zasu cinye mawakin saboda tsananin soyayya da suke nuna masa wanda hakan yakansa mutane mamakin cewa mata ma suna irin wannan nuna soyayyar to dai gashi an gani
Hakika kullum farin cikin hamisu breaker Kara yawa yake a wajen mutane kodan har yanzu yana wakoki masu ma’ana da kuma dadi ne shi yasa ana ganin babu wani mawaki bazai fito wanda zaifi hamisu breaker farin jini a wajen samari da kuma yan mata