Kamal Aboki na daukar sabon shiri da baturiya

Matashin jarumi kuma ɗan shirin barkwanci mai suna kamal aboki ya kara dauko wani sabon shiri wanda zai gabatar tare da farar fata wato baturiya wanda a duk lokacin da matashin ya saki sabon film akan nema domin akalla
Ya kware wajen bata mutane dariya da nishadantar dasu domin matashin yana kokari sosai wajen yin abinsa batare da yayi wani abin dazai jawowa kansa bakin jini ba
Kuma a tun lokacin daya saki tallan wannan shirin jama’a ke jira domin cikakken ya fito domin yadda ake tunanin zai kayatar da masu kallo ganin acikin shirin akwai baturiya
Kuma ya bayyana cewa amma fa shirin zai kasance me nisan zango ne kuma zai dauki lokaci yana gabatar da wannan shiri domin a kullum burinsa shine samun yawan masu kallo
Muna fatan wannan shirin Allah yasa a fara a Sa’a amma fa akwai ƙurar cewa wai wannan matar bafa ainihin baturiya bace kawai dai farar fata ce haka wasu mutanen suke zargi