LABARAI/NEWS

Kamfanin “SpaceX” ya samu amincewar gwamnatin Nigeria domin harba Network din sa ta cikin sararin sama mai suna “Starlink” a Nigeria”

πŸš€ Kamfanin “SpaceX” ya samu amincewar gwamnatin Nigeria domin harba Network din sa ta cikin sararin sama mai suna “Starlink” a Nigeria”πŸš€.


Kamfanin SpaceX mallakar wanda yafi kowa kudi a duniya “Elon Musk” kuma shugaban ‘yan Crypto, ya samu amincewar gwamnatin Nigeria na ya harba Network din sa dake amfani da “347 Air Space” a Nigeria, hukumar NCC ce ta bayyana haka jiya Juma’a, shi ma Elon Musk ya sanar a shafin sa na Twitter.
(Nace tow😳, MTN da Airtel Allah yaji kan ku).
Kamfanin SpaceX bai taba zuwa Africa da Network dinsa na Starlink ba, amma zai fara da zuwa Nigeria a matsayin kasa ta farko a Africa.

Kamfanin SpaceX da Network dinsa na Starlink shine kamfani kwaya daya na sadarwa da yafi kowanne karfi a duniya ta wajen karfin internet da saukin kudi wajen amfani a kasashen duniya.
Starlink yana aiki a kasashen duniya daban daban inda suke samar da internet ba tare da kafa wani karfe ko kafa wata Na’ura a zahiri ba, suna amfani da tauraron ‘dan Adam (Satellite) ne ta cikin sararin samani.
Amincewar da gwamnatin Nigeria tayi ma Starlink ya fara aiki ne daga jiya Juma’a, cikin wannan wata na May 2022.

Sai dai SpaceX bai fadi ranar da zai fara aiki a Nigeria ba, ko ranar da za’a fara ganin Network din sa a Nigeria, a hukumance dai gwamnatin kasar ta basu dama daga jiya, kuma Lasisin da aka basu na shekaru goma ne (10 Years), idan sun kare ana iya sabunta su (subject to renewal).
Starlink yana bada damar kiran waya ta internet Kai tsaye (ba irin wannan da muke yi na Gargajiya baπŸ˜€).
Sannan yana bayar da damar amfani da internet da Blockchain Technology Kai tsaye ta hanyoyi da dama (‘yan Crypto ga dama za’a kawo muku).

SpaceX sukan bayar da kula da taimako ma kowace kasa game da sha’anin tsaron ta hanyar Technology din Space 347.
Kamfanin yace yana fatan duk wani wajen da babu internet connection a Nigeria ya samar masa da internet din, kauye ne ko gari, tudu ko gangara, wajen da Network bai da karfi ko kuma gaba daya ma babu duk Starlink zai Kai zuwa wajen.
Da sauran abubuwa masu yawa.

SpaceX suna da cibiya a United States of America kuma suna aiki hannu da hannu da hukumar Binciken Sararin samaniya ta America wato “NASA”.
Network din Starlink ana samun sa a kasashe kamar haka:
US, Canada, the UK, France, Germany, Austria, the Netherlands, Ireland, Belgium, Switzerland, Denmark, Portugal, Australia da kuma New Zealand.

Elon Musk yayi nisa wajen kafa cibiyoyin sadarwa har acikin duniyar “Mars” dake gefe da duniyar mu ta “Earth” da zummar cewa nan gaba mutane da dama zasu koma rayuwa acan saboda matsalolin da wannan duniyar ke fuskanta, dan haka suke Sayan manyan filaye da yin gine a duniyar Mars da wasu duniyoyin da mutane suka Kai gare su.
Muna sauraren jin rana da lokacin da sadarwar Starlink zai fara aiki a Nigeria da yadda mutane zasu fara amfani dashi.

Daga : Abdul Hadi isa Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button