Daga Malaman mu

Kamin Ku Amince Da Auren Junanku Ku Tabbatar Da Wadannan Abubuwan

Kamin Ku Amince Da Auren Junanku Ku Tabbatar Da Wadannan Abubuwan:

 

Akasarin masoya da suke auren junansu babu abunda suka fi maida hankalinsu akai irin soyayyar da suke yiwa juna.

Wannan yasa idan akayi auren ba a jimawa ake rabuwa. Saboda soyayya kadai ba zai iya samar da zaman aure mai dorewa ba dole sai an hada da wasu abubuwa kamar haka:

1: Tabbatar Da Soyayyar Juna:

Dole ne kamin ku amincewa junanku zakuyi aure ya zamana kuna son junanku. Domin Shi addini na musulunci ya haramta yiwa namiji ko mace auren dole. Don haka soyayya shi ne abu na farko da zaku soma tabbatar wa junanku shi kamin kowa ya amince a daura aure.

2: Hakuri: Duk yadda kuke son junanku idan baku da hakuri da juna bafa zaku iya zaman aure ba.

Kashi 70 na zaman aure hakuri ne da juna. Kun yarda kun amince zaku iya hakuri da juna.

Muddin kuka tabbatarwa junanku hakan, to kuna iya daura aure. Amma idan guda cikinku yanada gajen hakuri, koda anyi wannan aure ba zai yi tasiri ba.

3: Fahimtar Juna: Shi ma wani abu ne da ya dace masoya su yiwa junansu kamin su amincewa juna aure.

Fahintar juna a zaman aure yana bada gagarumin taimako wajen dorewar zaman aure. Muddin masoya sukayi aure basu da fahimtar juna zargi da gulma na iya shigowa yadda zai iya yiwa auren nasu lahani.

4: Yarda Da Juna: Dole har sai masoya sun tabbatar da yarda a tsakaninsu kamin zancen aure ya biyo baya. Duk soyayyar da aka ginata akan rashin yarda haka nan za ayi zaman auren. Aure a rashin yarda kuma ba zai yi tasiri ba.

Dole ne masoya su kasance babu wani zargi da suke yiwa junansu komai kankantarta kamin su daura aure.

5: Yafiya: Idan kuda daga cikin ku ya aikata wani mummunar laifi zaku iya yafewa junanku kuma ku rufe zancen babu wanda yaji?

Wannan shima abun dubawa ne kamin masoya su amince a daura musu aure.

Wasu abubuwa suna iya faruwa a rayuwa da suke kama da azal ko kaddara, idan hakan ya samu da wanda kake aure ko kike aure zaki iya yafe masa ki hakura a kiyaye gama. Muddin har idan wadanda suke soyayya basu da zuciyar hakan to zaman aurensu na iya zama barazana gaba.

A zaman aure abubuwa suna faruwa daban daban kuma kala kala, wanda muddin ba halin mutum bane hakan ya zo a tsautsayi ne, sai a yiwa juna hakuri.

Ba manufa bane sai dole masoya sun tabbatar da wadannan abubuwan tsakaninsu kamin aure yake kasancewa tsakaninsu ba. Sai dai rashin la’akari da wadannan abubuwan suna yiwa Zamantakewan auratayya da dama illa.

Da fatan masoya zasu sasu cikin abubuwan da zasu maidasu ma’auni na neman aure ko na amincewa mai son aure.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button