Islamic Chemist

Kana Son Daina Istimna’i? To Kaga Hanyoyin Dena Wasa Da Al’aura Kwata-Kwata

Kana Son Dena Istimna’i? To Kaga Hanyoyin Dena Wasa Da Al’aura Kwata-Kwata:

 

Ina Tausayin

 

Duk talikin da yake fama da cutar wasa da al’aurarsa matuka, domin muddin yasan irin boyayyun illolin yin hakan ina da yakinin zaiyi kokari yaga ya dena.

 

To sai dai…

 

Irin wannan lamari nada wuyar dainawa, musamman idan mutum ya zama addicted (shine ko yaushe baya jin dadi ko gamsuwa sai yayi wasa da al’aurarsa).

 

Mai karatu ina maka barka da warhaka, kana tare da admin tsulum-tsulum a cikin sabon rubutu na mai taken “Yadda Zaka Daina Wasa Da Al’aurarka Hankali Kwance”.

 

Kaicon Wasu Iyayen, Lallai Kam Anji Kunya, ko kunsan me yasa? ina mamaki kwarai da gaske in har naga iyaye basa jawa yayansu maza kunne yayin da balaga ta fara riskarsu.

 

Mai karatu, zaka ga ‘ya mace da zarar balaga ta fara riskarta iyayenta zasu fara mata fada da nasihohi akan, rufe tsiraici, dena kule-kule maza, kame kai da sauransu.

 

Sai dai shi namiji ba kowadanne iyaye ke cika nuna tasu damuwar gareshi ba, lokacin da balaga ta fara riskarsa.

 

A garin haka maza ke fadawa wasa da al’aurarsu wai don su ragewa kansu sha’awa, hmm bo-no-no kenan.

 

Lokacin da mutum ya fara, zaiji shi kansa yana iya gamsar da kansa kwarai da gaske.

 

A hankali abin ke shiga jikinsa, tunaninsa da zuciyarsa ta haka har ya zama ya zama rabin jikinsa.

***************

Daga cikin irin illolin da wasa da al’aura ke haifarwa akwai irinsu:

 

❏ Kankantar Gaba.

❏ Rage Karfin Gaba.

❏ Saurin Inzali.

❏ Yawan Mantuwa.

❏ Yawan Karyewar Gashi.

❏ Yana Taba Idanu Ta Fannin Gani.

❏ Rashin Nutsuwar Zuci.

❏ Yana Haddasa Daukewar Sha’awa

❏ Yana Sawai Mutum Ya Daina Sha’awar Mace

❏ Yana Haifar Da Fushin Allah (S.W.T).

Wadannan sune kadan daga cikin irin illolin da wasa da al’aura ke haddasawa.

To mai karatu, a matsayinka na ‘dan adam, shin in Allah yayi fushi dakai waye kuma zai soka?.

Babu.

Haka kuma ina tunawa da gargadin masu wasa da al’aurarsu cewa: duk wanda ya mutu yana wannan ta’ada ya mutu dan wuta kuma mazinaci.

 

Domin ita ce ake kira da Zinar Hannu, in har a baya baka ji na fadi ba, yanzu kaji.

*****

Hanyoyi da kuma dabarun da zaka bi wajen ganin ka daina wasa da al’aurarka masu sauki ne, sai dai wuyar jurewa ga mai aikata istimnai.

 

Na farko dai ka sani, na sani, dole fa sai ka koma ga Allah mahaliccinka tukunna, in har kana son kaga komai ya dawo maka dai-dai.

 

Abubuwan Da Zaka Rinka Yi Domin Dena Istimna’i

Ka kudurta a zuciyarta, babu kai babu rike azzakarinka da zummar wasa dashi.

 

Ka dasa kyamar dukkanin wata mace mai fidda tsiraicinta, a cikin zuciyarka.

 

Kada ka yarda ka rinka karya tsarkin dake jikinka, ta hanyar fidda mani daga jikinka.

 

Ka yawaita karatun Al’qurani Mai Girma, domin karantashi na saka natsuwa da walwala cikin zuciya.

 

Kada ka rinka bari Sallah tana wuceka, ya kasance kana samun jam’i.

 

Ka kuma guji kwanciyar rub da ciki, domin in har zaka danne azzakarinka kana kallo ko wani abu ina mai tabbatar maka zaka iya cin karo da wani abu na tada sha’awa a cikin bidiyon

Kuma lallai-lallai ka daina zama a daki kai daya, ya kasance kowanne lokaci kana cikin jama’a (hakan zai kareka sosai).

 

Ka shafe tunanin ka taba wasa da azzakarinka daga cikin zuciyarka.

 

‘Dan uwa ka rinka yawaita Istigfari da neman gafara a wurin Allah (S.W.T), domin shi din mai gafara ne kwarai da gaske.

 

Ka kauracewa kallon duk bidiyon da zai tayar maka da sha’awa musamman bidiyon batsa.

A karshe ina tunasar damu da mu rinka tuna haduwar da Allah a kowanne lokaci, hakan zai rinka dasa mana shakka da tsoron aikata wadansu abubuwan.

 

In har nace, sai na rubuta dukkanin bayani akan wasu abubuwan, zamu ci lokaci sosai.

 

To amma mu tuna, yana da kyau in har zamu tuba, to ya kasance tuban har abada muka yi.

 

Banda tuban ‘yan kasuwa ko ‘yan siyasa, domin Allah (S.W.T) ba abun wasa bane.

 

Ya Allah, dukkanin wanda ke fama da wannan Allah dan girmanka, dan Ikonka ka rabashi da wanna masifa gaba daya.

 

Ina rokon duk wanda ya karanta wannan rubutu da yayi kokarin yin comment da Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

 

Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

 

Kayi comment da share na wannan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button