LABARAI/NEWS

Karfe Biyu Na Dare Gwamna Zulum Ya Dira Asibitin Monguno, Ya Karawa Likitoci Albashi Da Kashi 30%

Karfe Biyu Na Dare Gwamna Zulum Ya Dira Asibitin Monguno, Ya Karawa Likitoci Albashi Da Kashi 30%

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.

Baya ga likitoci, ma’aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma’aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.

Kananan hukumomin: Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki cikin Bama wanda suke daga cikin wuraren da ‘yan Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2014, ba tare da an zauna ba na kusan shekaru takwas har zuwa rufe sansanin ‘yan gudun hijara da masu neman mafaka aka yi.

Bulaliyar majalisar dattawa, Barr. Muhammad Tahir Monguno ne ya raka Zulum babban asibitin misalin karfe 1:00 dare suna can har zuwa karfe 2:00 dare.

Dr. Solomon Tiza, shugaban jami’an kiwon lafiya ne ya tarbeshi, gami da kewayawa dashi asibitn.

Gwamnan ya yi umarni da gina karin gidajen ma’aikata, samar da tuka-tuka da wutar Sola don bunkasa ayyuka a asibitin.

Da farko dai, a watan Janairu, 2022, Zulum ya daga albashin duka likitocin Borno zuwa matakin da gwanatin tarayya ke biya, don kawo karshen matsalar yadda likitocin jihar ke komawa asibitocin Gwamnatin Tarayya don samun albashi mai tsoka.

A shekaru ukun da gwamnan ya yi a mulki, ya amince da daukan ma’aikatan lafiya 676 wadanda suka hada da sama da likitoci 40 masu jinya 241, anguwannin zoma da sauransu.

Zulum ya kwana a Monguno, wanda ke arewacin jihar daga ranar Alhamis zuwa ranar Juma’a, don sauraran koken jama’a.

Gwamna ya je Monguno tare da Chief Muhammad Tahir Monguno, Kwamishinan gine-gine, da sake tsarin guri, Injiniya Mustapha Gubio, Kwamishinan Shari’a, Bari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button