LABARAI/NEWS

Karin Bayani akan ‘Mutum 7 sun mutu a harin jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna’

Mutum 7 sun mutu a harin jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna’

Bayanai sun tabbatar da cewa an sace mutane da dama sannan aka kashe wasu

Majoyoyi daga asibitin 44 na Jihar Kaduna da aka kai wasu daga cikin mutanen da harin da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun ce mutum bakwai ne suka mutu.

Kazalika sun ce mutum ashirin da biyu suka jikkata.

Wakilin BBC da ya kai ziyara asibitin, Yusuf Tijjani, ya ce ana kula da mutanen da suka jikkata a sashen bayar da kulawar gaggawa na asibitin.

A cikin wadanda aka harba kuma suke jinya a sibitin har da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Mohammed Ibrahim Wakkala.

Hukumar Kula da Safarar Jiragen Kasa ta Najeriya ta dakatar da jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.

A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita da safiyar nan, ta ce “saboda wasu dalilai da ba mu shirya musu ba, mun dakatar da jigilar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna. Nan gaba za mu yi muku karin bayani idan akwai”.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace wasu fasinjoji da ba a bayyana adadinsu ba daga wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin.

Shaidu sun ce jirgin ya kauce daga kan hanyarsa bayan fashewar wani abu a kan hanyarsa.

Rahotanin sun ce an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata.

An kai wa jirgin kasan mai dauke da fasinjoji kusan 1,000, harin ne da misalin karfe 8 na dare.

Fasinjoji da kuma ‘yan uwan wasu fasinjojin sun shaida wa BBC cewa lamarin ya yi matukar muni kuma har yazu ba a san takamaiman mutanen da lamarin ya shafa ba.

Wani fasinja ya shaida mana cewa bayan jirgin ya tsaya, ‘yan bindiga sun kewaye shi tare da bude wuta.

Mutane sun sunkuya kasa domin samun mafaka kuma daga nan ne maharan suka nufi hanyar jirgin, inda suka harbe fasinja daya a kusa da inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, in ji shi.

“Muna cikin tafiya kawai muka ji abu ya yi kara, bam ya tashi ya girgiza sannan kuma muka ji karar harbe-harbe, bayan an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ke cikin jirgin Allah ya taimake mu jami’an tsaron sun fi karfin su amma duk da haka sun kwashi wasu mutane a ciki”, a cewar sa.

Wani fasinjan da ke cikin jirgin ya ce an samu asarar rayuka.

Ya ce sun kashe mutum guda. “Mun ji ƙarar harbe-harbe, muna cikin tashin hankali,” in ji shi.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an tura sojoji domin ceto fasinjojin tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

Yawaitar kai hare-hare da sace-sacen mutane da ake yi a babban titin Abuja da Kaduna ce ta sa matafiya da yawa suka gwammace yin tafiya ta jirgin kasa.

Sai dai wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari kan hanyar jirgin cikin watanni shida da suka wuce.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button