Fadakarwa

KARKU SAKANKANCE DA KOWA AKAN YARANKU

KARKU SAKANKANCE DA KOWA AKAN YARANKU
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Zamani ya ɓaci yanzu hatta iyaye akan samu masu haikewa yayansu da sunan sha’awa, wasu harma sukai ga su suka fara lalata yaran BA kuma cikin musulmai ba ko wadanda ba musulmai ba, wannan masifar ko wadanne rukuni ansha kama wasu da ita.

Ballantana agangara azo kan yan uwan juna zaka samu Wane ke lalata kannensa.

Kwai wanda ya kamu da kanjamau wanda saida ciwon ya kawosa gargara sannan likitoci suka fahimtar da mahaifiyarsa… bayan ya rasu cikin kannensa uwar ke bayanin abunda ya kashesa hankalin kannen ya tashi ashe duk ya ɓatasu suma.

Haka tsakanin yan uwan dangi cousin-cousin wasu suna cin karensu ba babbaka

Toh yanzu abun bai bar har yan kananun yaran mu masu shekaru 3 zuwa 12 ba.

Wasu mazajen ko bunsuru ya fisu mutunci ade irin halayyar da suke. Ƙananun yara zaka samu suna yiwa ƙwaqule koma su haike musu su ɓata musu farji su bar yaran na fama da azaba tare mugun infection, gami da illar da shikenan har mutuwarsa sun sa musu mugun tabo.

Kai ba yara Mata ba yanzu bala’in yakai har kananun yara Maza yan shekara 5 zuwa 8 gashinan luwadi ake abata musu dubura abarsu da tsutsotsi na sukarsu tare da tsikarin duburarsu ba’a sani ba saboda a zuba musu ruwan maniyyi a dubura yai kwanaki, dare yai yaro ya kasa bacci

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

BABBAN JAN HANKALIN ANAN SHINE

■- Iyaye Mata kune kuka fi kusa da yaran nan, kune ke tare dasu ko YAUSHE! lallai kuma tilas-tilas-tilas kunji na maimaita har sau 3 ko? DOLE ne inde kin kasance uwa ta gari toh ki koyi jawo yaranki ajika kike nuna ke abokiyarsu ce! Karsu ɓoye miki komi… suke gaya miki duk abunda ya samesu… ko wani ne yake kama jikinsu kice su fadamiki.

Hakan kuwa baza kici nasarar samu su saki jiki suke miki bayani ba sai kin sauko da kanki ƙasa daidai su. Ki kokarin gaske ki sami yardar ƴayanki ta yadda baza suji nauyin fadamiki komi ba kada ya zamto kullum ke da su sai zare ido.

Haka in sun fadamiki kike reacting cikin hikima da nutsuwa kada ki hau musu masifa baababababa sai kace zaki cinyesu, kina zagi hakan zaisa bazasu ƙara fadamiki wata matsala ba duk yadda zaki kuwa.
Musamman in me cin zarafin nasu ya zamto yana tsoratasu da insuka fadama wani sai ya yanka su.

■- Karki yadda da kowa agame da yaranki musamman Mata ko waye. Eh ko waye! Kisa ido akansu sosai, koda tsakaninsu ƴaƴan ki Maza muddin ba kina da tabbacin tarbiyarsu ba ballantana ga wani baƙo

■- Banda barinsu suna fita waje anyhow su kaɗai. A Nigeria ne kurum zakaga yaro shi kadai na yawo bawani babba tare dashi saboda tsabar sakaci. Don haka ko makaranta suka fita kike laƙantar a yaya suka fita ya kuma aka dawo!

Duk randa kika fara ganin ana dawo miki da hijabi ahannu ko wando, ko ɗankwali ko takalma ahannu a hargitse kila fuska duk jirwayen hawaye.. ki kokari ki binkici ya akai ki takama abun birki koda da yayyensu suke tafiya kuwa. Lallai ki nutsu.

■- Ki rika yi Musu addu’a kina shafa kansu, suke ji da kunnensu duk sanda zasu fita kina musu addu’a… ki kuma ce suma suyi, sannan ki ce Allah tsareku, yasa adawo lfy.

■- Kice musu banda hawa ko zama jikin kowa inba babansu ko jikinki ba, sannan baki yadda da wasan amarya da Ango ba. Kul

■- Ki sani duk wani abu da zakiga sunyi na rashin gaskiya ko kuskure tohfa Kada kurum kice kai uwaku ku bar abin nan… Shi yaro inkikace yabar abu kurum batare da masa bayani ba tohfa saide yabar yin abin nan akan idonki amma ba fasawa yake ba. Kuma zaita tunani da saƙe-saƙe meyasa Mama bataso nai kaza.

Don haka idan kika kwaɓi yaro abu toh ki qara da bayani, ai nace karkayi ne saboda wannan abin kaza da kaza ne, kaji irin makomar me yi. Hakan zaisa bazai kuma yi ba, inyaji wani yayi toh shima me kwabarsa ne.

■- Kike zaunar dasu kina basu labarai da tarihin mutanen kwarai da irin abubuwa na rashin daɗi dake samun wanda ya kauce hanyar Allah. Ki nuna musu irin tausayi da jin kai na ubangiji, yadda yake bada lada ga yara masu biyayya, da basa ɓoyewa iyayen su komi saboda gaskiya, kita faɗamusu labarin aljanna da abubuwan ciki, kice kunga irin abu kaza na film kaza ai na aljanna ya ninka haka.

Ko yaushe de kike nunawa yara Allah me jin kai ne, ba yawan zancen azabar sa ba. Ki kuma faɗamusu albarka bin iyaye da rike gaskiya.

■- Abu na karshe shine KUL kika zamo WAWUYAR UWA… wacce yaro xai zo yana kuka amma kafin ma ya fara bayani kin datseshi kin hau yi masa ko mata faɗa cewa toh sarkin kuka, shege, yi mun shiruuuuuuu nan banza kawai. Wawiya kurum ke wannan, inkina haka toh Allah ya kiyaye… Randa wani abun zai bayyana kece zaki kukan. Yaro baiwa abu guda kuka iri ɗaya kullum, inbaki jasa ajika bazaki fahimta ba.

Rashin sauraron yaron ba karamin rashin hankali bane, infact manyan matsalolin ta nan suke farawa… kila wani yai molesting din yarki tazo tanason fadamiki amma bataga fuska ba saboda shirmenki na rashin iya mu’amala…. don haka inde kina da wannan halin maza maxa ki canza. Ki zamo GOOD LISTENER na yaranki…. Hakan shi zaisa su saki jiki su fadamiki komi.

Don haka iyaye ku kiyaye wannan… Allah kuma ya tsare mana zuri’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button