LABARAI/NEWS

Kasar Chana ta Bude Ofishin Yan Sanda a Najeriya

Kasar Chana ta Bude Ofishin Yan Sanda a Najeriya.

Gwamnatin kasar Sin ta bude ofisoshin ‘yan sanda a Najeriya da kuma a kasashe sama da 20 na Turai da Amurka da Asiya da Afirka a kokarin da take yi na magance yawaitar ayyukan ta’addanci da ‘yan kasar ke yi a kasashen waje.

Wannan yana kunshe ne a cikin wani rahoton bincike da kasar sin ta fitar.

A cikin rahoton binciken an ba da rahoton cewa an ƙirƙiri ofisoshin ‘yan sanda ne don murkushe duk wasu nau’ukan haramtattun ayyuka da aikata laifuka da suka shafi Sinawa a kasashen ketare.

Kasashe irin su Lesotho da Tanzania kasashe biyu ne a Afirka da ke da ofisoshin ‘yan sandan kasar Sin, baya ga Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button