Daga Malaman muFadakarwaGirki Adon Uwargida

Ki Kiyaye Wadannan Abubuwan Idan Kina Son Ki Tsufa Da Nonuwanki A Mike

Ki Kiyaye Wadannan Abubuwan Idan Kina Son Ki Tsufa Da Nonuwanki A Mike

Ki Kiyaye Wadannan Abubuwan Idan Kina Son Ki Tsufa Da Nonuwanki A Mike:

 

Nonuwa a jikin mace bangarene da suke karama kyau da kuma jawo hankalin miji domin motsa masa sha’awa.

Duk da yake akwai matan da a hlittance basu da nonuwa masu girma, amma saboda ci gaban zamani suna iya karawa nonuwan su girma ta hanyoyi da dama. Akwai kuma wasu matan da sunada halitta na nonuwa tsayayyu, amma saboda rashin kula dasu suke zubewa tamkar wacce ta rayate silifas.

Idan kika kiyaye wadannan abubuwan, ba yawan haihuwa har tsufa sai kiyi da nonuwanki gwanin sha’awa.

1: Ki Yawaita Shan Sinadarin Bitamen C da B:

Su wadannan sinadaren suna gyarawa mace jikinta musamman kuma nonuwanta. Lemun tsami da irinsu mangwaro duk sinadare ne dake gyarawa mace nonuwanta.

2: Cin Kayan Da Zasu Kara Kina: Ba ana nufin kiyi ta cin abunda zai kara miki jiki kiyi tim ba.

Ki rika cin abinci da ke gina jiki saboda nonuwa suna girma ne a lokacin mace take kara jiki suma suna kara girma.

3: Ki Guji Rama: Muddin zaki kiyayya nauyinki kada kiyi girma dayawa kada kuma ki rame zaki tsufa da nonuwanki garau.

4: Duk matar da take son ganin ta tsufa da nonuwanta a mike ta guji shan taba sigari. Taba sigari yana iya fatan jikin mace illa inda nan take sai saka jiyojin da suke rike da nonuwa su sake.

5: Akwai man shafawa na musamman da ake sayarwa ko hadawa domin shafawa nonuwa fata da jijiyoyin wajen su tsaya gam.

  • MAN ZAITUN
  • MAM KWAKWA
  • MAN HULBA
  • MAN RIDI
  • MAN HABBA.

6: Yawan Motsa Jiki:

Shima hanya ne dake taimawaka mata su tsufa da nonuwansu. Duk macen da take yawan motsa jikinta idan aka ganta za a ga nonuwanta akwai mamora ba kamar macen mai son jiki ba.

Saboda motsa jiki yana saka jini ya kwarara zuwa nonuwan mace yadda zai taimaka musu wajen karin lafiya.

7: Rage Shiga Rana:

Duke da yake nonuwa suna cikin rigansu kuma a rufe da taguwa. Yawan bayyanasu cikin rana ya iya fatan dake rike dasu da kuma jijiyoyin sagewa.

Don haka duk macen da take son nonuwanta su dau hankalin mijinta ko ta tsufa, ta rage baza su a rana. Yawan sasu cikin dohu da kuma zafi yana kara musu lafiya.

8: Yawan Shan Ruwa:

Shima yakan taimaka wajen gyaran nonuwaan mace.

Idan mace zata rika shan ruwa akai akai a kullum za aiya ganin nonuwanta a wadace koda kuwa ta killacesu ne.

Kaman ko ina na jikinki, nonuwanki suna son kula na musamman, domin suna daya daga cikin abunda maza ke zumudi auren mata masu kananan shekaru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button