LABARAI/NEWS

Kimanin Ƴan Takara Tara Ne Suka Ajiye Batun Takarar Su ….. Yayinda Aka Dakatar Da Kaɗa Ƙuri’a Saboda An Tada Hargitsi..

Kimanin Ƴan Takara Tara Ne Suka Ajiye Batun Takarar Su ….. Yayinda Aka Dakatar Da Kaɗa Ƙuri’a Saboda An Tada Hargitsi..

A yayin da ake ci gaba da ƙoƙari fidda Ɗan Takara Ɗaya Tilo da zai wakilci Jam’iyyar APC a Babban Zaɓe mai zuwa Kimanin ƴan takara Tara ne dai suka janye takarar su tare da goyama wasu ƴan takarar baya.

Waɗannan ƴan takarar sune suka janye domin marawa Tinubu baya.

1- Sen. Goodwill Akpabio
2- Sen. Ibikunle Amosun
3- Gov. Kayode Fayemi
4- Rt. Hon. Dimeji Bankole
5- Sen. Ajayi Borofice
6- Gov. Badaru Abubakar
7- Prof. Ben Ayade

Yayinda Nicholas ya janyema Farfesa Osibanjo, Pastor tunde bakare kuma ya bayyana cewa bai shiga takara Dan ya janyema wani ba daɗin daɗawa ma yace Buhari ne yabashi ƙwarin guiwar tsayawa takara kuma yace yanada Natsuwa da shi zai iya Damƙa mashi ƙasar domin samun ci gaba.

Tun dai wajen ƙarfe Biyu da Rabi na dare aka dakatar da kaɗa ƙuri’a saboda Hargitsi da wasu suka tada Lamarin da yayi sanadiyyar ya mutsewar filin taron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button