LABARAI/NEWS

Kisan Hanifa: Kotu ta tabbatar da ikirarin Tanko kan cewa shi ya kashe Hanifa

Kisan Hanifa: Kotu ta tabbatar da ikirarin Tanko kan cewa shi ya kashe Hanifa.

Dan Bala

Babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Naabba ta tabbatar da cewa jami’in ‘yan sanda mai bincike Sajan Lurwan Ibrahim ya nadi bayanan ikirari na wadanda ake zargi da kashe Hanifa wato Abdulmalik Tanko da Fatima Jibril Musa bisa radin kansu, ba tare da wata barazana ko tursasawa ba kamar yadda lauyan masu kare su ya yi zargi.

Jarida Radio a baya ta ruwaito cewa babban lauyan dake kare wanda ake tuhuma, Barista Mukhtar Usman Kabo ya bayar da hujjar cewa bayanan ikirari na Abdulmalik da Fatima suka bawa yan sanda, sunyi ne ta hanyar tursasawa, barazana da kuma tsoratarwa.

A yayin ci gaba da shari’ar a yau, Sajan Lurwan Ibrahim ya shaida cewar ya nadi bayanan tanko da fatima cikin yanayi mai kyau ba tare da ababen da aka zarge su ba.

Da aka yi masa tambayoyi, ya musanta cewa ya firgita wanda ake tuhuma kafin ya samu bayanan nasu.

“a ofishin mu aka mafi bayanan a gaban abokan aiki na, har da busawar fanka da hasken lantarki a sanda suke gabatar da jawabin su”. inji shi

Hakazalika a shedar da suka bayar daban-daban a lokacin da ake shari’a, Sajan Muhammad Yanfa da ASP Sani Hussaini Kyarma, sun shaida wa kotun cewa, an sami bayanan su ne da radin kansu wanda sukai ikirarii aikata kisan, kuma jawabin nasu Abdulmalik da Fatima an sake shi ne ba tare da gallazawa, barazana, tsangwama ko tursasawa ba.

A hukuncin da ya yanke a ranar Laraba, Mai shari’a Usman Naabba ya ce bisa ga hujjojin da aka gabatar a gaban kotun nasa a lokacin da ake ci gaba da shari’ar, shari’a ta tabbatar da cewa an nadi bayanan ikirari guda 2 ne bisa radin kansu ba tare da wata tsangwama, tursasawa ko azabtarwa ba.

” Na fahimci Sajan Lurwan a matsayin mai kwazo kuma amintaccen shaida. Na yarda cewa akwai mutane da yawa a ofishin lokacin da aka dauki bayanan wadanda ake tuhuma “

“Lauyan wanda ake tuhuma bai girgiza shaidu ba, kuma bai saba wa bayanan da shedun ‘yan sanda 3 suka bayar ba a shari’ar”

Alkalin kotun ya ci gaba da cewa, shaidar Fatima ta nuna cewa ba a yi mata duka ba, amma ta yi mata barazana.

Ya ci gaba da cewa, Abdulmalik ya kasa ambato dan sandan da ya fito da shi daga kurkuku ya azabtar da shi.

“Na yi nazari sosai kan shaidar kuma na yi imanin cewa an samu bayanan ikirari ne da raɗin ran su ba tare da tursasawa ba, ko kuma barazana.

Mai shari’a Na-abba ya dage zamansa zuwa ranar 22 ga watan Maris domin ci gaba da sauraron karar.

Jarida Radio
9/3/22

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button